Sarkin Musulmi Ya Kawo Hanyar Magance Rikicin Manoma da Makiyaya

Sarkin Musulmi Ya Kawo Hanyar Magance Rikicin Manoma da Makiyaya

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi ya buƙaci makiyaya su rungumi tsarin kiwo na zamani domin rage rikice-rikice da manoma a fadin kasar nan
  • Ya yabawa jami’an ‘yan sanda kan ƙoƙarin da suke yi wajen yaƙi da 'yan ta'adda yayin da suka kai masa wata ziyara ta musamman
  • Sarkin Musulmin ya kuma gana da jami'an hukumar shige da fice inda ya buƙaci gwamnatin tarayya ta samar masu da kayan aiki na zamani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya gana da mataimakin sufeton 'yan sanda mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, DIG Sulaiman Muhammad Abdul, a fadarsa da ke Sokoto.

DIG ɗin ya kai ziyarar ne tare da kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa, domin ganawa da Sarkin Musulmi.

Kara karanta wannan

'Kashi 80 na matsalolin tsaro da suka addabi Sakkwato na da alaka da miyagun kwayoyi'

Sarkin Musulmi da 'yan sanda
Mai alfarma Sarkin Musulmi na ganawa da jami'an 'yan sanda a fadar shi. Hoto: Jama'atu Nasril Islam Nigeria
Source: Facebook

Shafin JNI ya wallafa a Facebook cewa daga cikin dalilan ziyarar akwai ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da masarautun gargajiya.

Batun rikicin manoma da makiya

A yayin ganawar da ya yi da jami’an ‘yan sanda, Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin tsaron al’umma da haɗin kan jama’a wajen yaƙi da matsalolin tsaro.

Sarkin Musulmin ya shawarci makiyaya da su rungumi tsarin kiwon shanu na zamani ta hanyar kafa wuraren kiwo na dindindin domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da ake samu tsakanin manoma da makiyaya.

Ya kuma yaba wa rundunar ‘yan sandan Najeriya kan ƙoƙarin da take yi wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.

Sultan ya yi addu’ar Allah Ya ba jami’in ɗan sanda Abdulrazak Muhammad lafiya cikin gaggawa bayan ya samu raunuka a wani artabu da ‘yan bindiga a Tureta.

Sarkin Musulmin ya kuma roƙi Allah Ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a jihar Sokoto da kuma Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

A wata 1 kacal, hukumar kwastam ta tara kudin shiga sama da Naira biliyan 100 a tashar TinCan

Sarkin Musulmi ya gana da jami'an NIS

Mahalarta kwas na kwalejin horar da manyan jami’an hukumar shige da fice ta Najeriya da ke Sokoto sun kai ziyara fadar Sarkin Musulmi.

Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya buƙaci gwamnatin tarayya ta samar wa hukumar kayan aikin zamani masu inganci.

Ya yaba wa hukumar shige da fice kan rawar da take takawa wajen kare iyakokin Najeriya da kuma fuskantar sababbin barazanar tsaro.

Sarkin Musulmi da jami'an NIS
Lokacin da jami'an NIS suka ziyarci Sarkin Musulmi a Sokoto. Hoto: Jama'atu Nasril Islam Nigeria
Source: Facebook

Sarkin Musulmin ya bayyana cewa samar da kayan aiki na zamani da kuma ci gaba da horar da jami’ai na da matuƙar muhimmanci wajen inganta ƙwarewa.

Ya yi Allah wadai da ayyukan ‘yan bindiga da sauran nau’o’in laifuffuka, yana mai cewa addinin Musulunci bai amince da tashin hankali ko kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba.

Kwayoyi ke kara matsalar tsaron Sokoto

A wani rahoton, kun kawo muku cewa Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya yi magana kan rashin tsaro da ya addabi jihar tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

An fara sabuwar fafutukar neman karin albashi mai tsoka a Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya bayyana wa jama'a cewa kaso 80 na matsalolin tsaron jihar Sokoto na da alaka da shan kwaya.

Jihar Sokoto da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta dade tana fama da matsalolin tsaro da suka jawo garkuwa da mutane da rufe makarantu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng