Rundunar soji ta gano hanyar da Boko Haram ke dibar ma’aikata a shafukan zumunta
Rundunar sojin Najeriya a raar Talata ta ce ta gano wani shafin Facebook da sauran shafukan zumunta da kungiyar Boko Haram ke amfani da shi wajen diban sabbin mambobi.
Manjo Murtala Usman, kwamandan Operation Lafiya Dole, wanda ya bayyana hakan yayinda yake Magana a taron tallafin horo da ake yi a Maiduguri, yace shafukan zumuntan na da mabiya 2,000.
Usman ya bayyana cea yan ta’adda daga bangaren Albarnawi na Boko Haram na daukar sabbin mambobi a shafukan zumunta irin su Facebook, WhatsApp, SnapChat, Instagram da Youtube.
Yace rundunar sojin sun gano hakan ne yayin da suke tambayoyi ga babban Kwamandan Boko Haram mai suna Malu-Mamman Barde, wanda aka bibiyaa aka kuma kama a kudancin yankin Rann dake karamar hukumar Kala-Balge dake Borno.
KU KARANTA KUMA: Zan kawo karshen kashe-kashe idan aka zabe ni shugaban kasa - Makarfi
Barden a daga cikin manyan yan Boko Haram da suka aikata laifuka da dama.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng