Jirgin Shugaban Isra'ila Ya Yi Karo da Garken Tsuntsaye a Sararin Samaniya
- Jirgin saman da ke dauke da Shugaban kasar Isra'ila, Isaac Herzog ya yi saukar gaggawa bayan wani garken tsuntsaye ya buge shi a sama
- Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Isra'ila ya gaggauta sauka daga jirgin a lokacin da abin ya faru yana tsaka da tafiya zuwa wani waje
- A wani jawabi da ya yi, Herzog ya sake kira da a aiwatar da shirin shugaban Amurka, Donald Trump kan sake gina Gaza kwace makaman Hamas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Isra'ila - Jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojin saman Isra'ila da ke dauke da shugaba Isaac Herzog ya yi saukar gaggawa a ranar Alhamis bayan ya yi karo da garken tsuntsaye a yayin da yake shawagi.
A cikin wata sanarwa, rundunar sojin Isra'ila ta ce jirgin yana dauke da Herzog ne daga wajen bikin tunawa da wadanda suka mutu a Dutsen Herzl da ke Kudus zuwa Arewacin Isra'ila.

Kara karanta wannan
'Dan majalisar Amurka ya fadi kokarin da ya yi don kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya

Source: Getty Images
Rahoton da Roya News ta wallafa ya nuna cewa lamarin ya faru ne yana dawowa da wajen da ya kai ziyarar ta'aziyya ga mutanen da ke zaman makoki.
Jirgin Isra'ila ya samu matsala
A lokacin tashin jirgin, wasu tsuntsaye sun buge shi, lamarin da ya tilasta masa sauka a sansanin sojin saman Palmachim da ke tsakiyar Isra'ila.
Sai dai duk da saukar gaggawa da ya yi, rundunar tsojin kasar a ce ba a samu wata lalacewa ko rauni sakamakon aukuwar lamarin ba.
An bayyana cewa Herzog da ma'aikatan jirgin sun koma cikin wani jirgin sama mai saukar ungulu daban sannan suka ci gaba da tafiyarsu kamar yadda aka tsara.
Sojojin Isra'ila sun ce an mika jirgin da abin ya shafa ga kwararrun masu kula da jiragen sama na rundunar domin a yi masa gyare-gyaren da suka dace domin mayar da shi aiki cikin gaggawa.
Sun kuma ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan abin da ya faru, yayin da fadar shugaban Isra'ila ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan lamarin ba.

Source: Getty Images
Maganar Herzog game da Gaza
Tun da farko a wajen bikin tunawa da shekaru 12 da yakin Gaza na shekarar 2014, Herzog ya ce wajibi ne Isra'ila ta ci gaba da aiwatar da shirin Shugaban Amurka, Donald Trump na sake gina Gaza.
Ya ce yakin na 2014 ne ya kasance farkon jerin abubuwan da suka jawo rikice-rikice masu tsawo da radadi, yana mai cewa tunanin wadanda suka mutu a yakin na ci gaba da kasancewa a zukata Isra'ilawa.
Times of Israel ta wallafa cewa Herzog ya kuma yi ikirarin cewa a halin yanzu sojojin Isra'ila suna iko da kusan kashi 60 cikin 100 na yankin Zirin Gaza.
Tsuntsaye sun tsorata Trump
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya tsorata da ya hango tsunsaye a saman shi a White House.
Trump ya nuna alamun ya firgita bayan wucewar tsuntsayen, inda ya ce ya yi tsammanin hari aka kawo fadar shugaban Amurka.
Lamarin ya faru ne a lokacin da Donald Trump ke kai hare-hare Iran bayan kama Shugaban kasar Venezuela, abin da ya sanya shi zaman dar-dar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
