Da Gaske Tsohon Gwamna Ya Mutu a Najeriya? Gwamnatin Delta Ta Tsage Gaskiya

Da Gaske Tsohon Gwamna Ya Mutu a Najeriya? Gwamnatin Delta Ta Tsage Gaskiya

  • Gwamnatin Delta ta yi karin haske game da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan jihar ya rasu
  • Wasu rahotanni sun yada cewa Emmanuel Uduaghan ya rasu a jiya Laraba 24 ga watan Yunin 2026 wanda a tayar da hankula
  • Gwamnatin ta yi kira ga jama'a su daina yaɗa labaran da ba a tantance ba, tana mai cewa irin waɗannan jita-jita na jawo wa iyalai damuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Gwamnatin Delta ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar ya mutu.

An yi ta yada cewa tsohon gwamnan jihar, Emmanuel Uduaghan, ya rasu wanda ya tayar da hankulan al'umma a jihar.

Gwamnatin Delta ta karyata mutuwar tsohon gwamna
Gwamna Sheriff Oborevwori da tsohon gwamna, Emmanuel Uduaghan da ake yada rasuwarsa. Hoto: Rt Hon. Sheriff Oborevwori.
Source: Facebook

An bayyana hakan ne ranar Laraba ta bakin Babban Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai ga Gwamna Sheriff Oborevwori, Ossai Success wanda ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

A wata 1 kacal, hukumar kwastam ta tara kudin shiga sama da Naira biliyan 100 a tashar TinCan

Gwamnatin Delta ta karyata mutuwar Uduaghan

Hadimin gwamnan ya ce ya tuntubi iyalan tsohon gwamnan domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

A cikin saƙo da ya wallafa mai taken "Tsohon Gwamna Uduaghan Yana Raye – Jita-jitar Mutuwa Ƙarya Ce," Ossai ya ce ya yi magana kai tsaye da diyarsa, Orode Uduaghan.

Ya bayyana cewa bayan ganin rahotannin da ke ikirarin mutuwar tsohon gwamnan, mutane da dama sun tuntube shi suna neman tabbatar da sahihancin labarin da ke yawo.

Ossai ya ce nan take ya tuntubi iyalan Uduaghan domin samun tabbaci, ya ce Orode Uduaghan ta tabbatar masa ta wayar tarho cewa mahaifinta yana cikin ƙoshin lafiya.

Ya rubuta cewa:

"Na yi magana kai tsaye da diyarsa Orode Uduaghan, kuma ta tabbatar min cewa labarin ƙarya ne. Dr. Uduaghan yana raye."
An yada labarin mutuwar tsohon gwamnan Delta
Taswirar jihar Delta da aka ce tsohon gwamna ya mutu. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da yada jita-jitar mutuwa ke haddasawa

Hadimin gwamna Sheriff ya nuna takaicinsa kan yadda wasu ke yaɗa bayanan da ba a tantance ba, yana mai kira ga jama'a su kasance masu kula kafin su raba labarai.

Kara karanta wannan

Babbar mota ta burma kan 'yan APC suna tafiya kamfen, an samu asarar rai

A cewarsa, yaɗa jita-jitar mutuwar mutum abu ne mai muni saboda yana haddasa baƙin ciki da damuwa ga iyalai da abokan arziki.

Ya ƙara da cewa:

"Yaɗa labarin ƙarya kan mutuwar mutum zalunci ne kuma rashin tausayi ne, domin yana jawo damuwa ga iyalansa da kuma al'umma."

Ossai ya bukaci jama'a su yi watsi da rahoton, su kuma guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, ya jaddada cewa Emmanuel Uduaghan yana cikin ƙoshin lafiya kuma bai rasu ba.

Hadimin gwamnan Delta ya rasu a wurin taro

A wani labarin, an ji cewa an tabbatar da mutuwar babban mai tsara ayyukan gwamnan jihar Delta, Sunday Kotor bayan ya yanke jiki ya fadi a wurin taro.

Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi alhinin rasuwar Sunday Kotor tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalai da sauran 'yan uwansa.

Rahoto ya nuna cewa marigayin ya fadi ne a wani taro da ya shirya na kashin kasa, likitoci suka tabbatar da ya mutu bayan an garzaya asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.