Gaskiyar lamari PDP bata da niyar chanja suna - Lamido

Gaskiyar lamari PDP bata da niyar chanja suna - Lamido

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Sule Lamido, yace jam’iyyar bata da niyar chanja sunanta.

Ya ce PDP ba hawainiya bace da zata chanja sunanta don kawai ta cika burin wadanda ke son shigarta.

Da yake Magana a garin Minna yayinda yake jawabi ga tawaga akan taron jam’iyyar na wata mai zuwa, Lamido yace duk wanda bai aminta da sunan jam’iyyar ba toh ya tattara kayansa.

Gaskiyar lamari PDP bata da niyar chanja suna - Lamido
Gaskiyar lamari PDP bata da niyar chanja suna - Lamido

Akwai fafutukar da gammayar kungiya ke yin a ganin an chanja suna da alamar PDP domin kwace mulki daga hannun jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

KU KARANTA KUMA: Almubazaranci a yayin aure ke haddasa mutuwar aure - Sultan

Yace barnar da gwamnatin APC tayi ya kawo koma baya a kasar ya kara da cewa lamarin tsaro a fadin kasar ya tagayyara.

Tsohon gwamnan na jihar Jigawa yaace APC na cike da tsoro saboda kwakwalwar jam’iyyar sun sauya sheka zuwa PDP sannan kuma a yanzu basu da karfin gwiwa jawo hankalin yan Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng