Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Bulla a Arewa

Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Bulla a Arewa

  • Ana cikin kokarin magance kungiyoyin Boko Haram, Lakurawa da ISWAP, an samu bullar wata sabuwar kungiyar ta'addanci a jihar Kebbi
  • An tabbatar da mambobin kungiyar suna gudanar da ayyukansu a karamar hukumar Argungu, wanda hakan ya jawo fargaba kan tsaro a yankin
  • Majiyoyi sun bayyana cewa kungiyar ta Sai Malam ta dade tana harkokinta ba tare da hankalin hukumomin tsaro ya kai kansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta yi magana kan kan bullar wata ƙungiyar asiri mai alaƙa da ta'addanci mai suna ‘Sai Malam’.

Gwamnatin ta bayyana cewa kungiyar na gudanar da ayyukanta a yankin karamar hukumar Argungu da ke jihar.

Kungiyar 'yan ta'adda ta bulla a Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, na jawabi a wajen taro Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Mai bada shawara kan al'amuran tsaro na jihar, Kanal Danladi Ribah mai ritaya, ya bayyana hakan ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026, jaridar Tribune ta kawo rahoton.

Sabuwar kungiyar ta'addanci ta bulla a Kebbi

Tsohon sojan ya bayyana hakan a lokacin wani taron tattaunawa tsakanin mataimakin babban sufeton 'yan sanda na kasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma (DIG), Suleiman Muhammad Abdul, da masu ruwa da tsaki kan al'amuran tsaro a Birnin Kebbi.

Kanal Danladi Ribah ya ce an fara gano ƙungiyar ne a jihar Sokoto, inda hukumomin tsaro suka samu nasarar daƙile ayyukansu.

To sai dai kuma, ya nuna damuwa kan bullar ƙungiyar a wasu sassan jihar Kebbi, inda ya ce gwamnatin jihar tana tattaunawa da hukumomin tsaro domin shawo kan lamarin kafin ya kazanta.

“Ba tare da wata shakka ba, mabiya ƙungiyar Sai Malam suna nan da yawa a Argungu. A baya an gano su a Zuru, amma ba su da yawa."

- Kanal Danladi Ribah

Wace kungiya ce 'Sai Malam'?

Ƙungiyar Sai Malam wata ƙungiyar asiri ce mai alaƙa da ta'addanci wadda aka ce ta yi aiki a wasu sassan jihar Sokoto kafin ta ɓullo a wasu yankunan jihar Kebbi, rahoton jaridar Daily Trust ya nuna hakan.

Sakamakon ayyukansu, an ruwaito cewa an kama shugabansu da wasu manyan mambobinsu a Sokoto.

Sai dai kuma, rahotanni sun nuna cewa wasu tsirarun ɓangarorinsu sun sake haɗuwa a yankin karamar hukumar Argungu.

Gwamnatin jihar Kebbi tana fargabar shigowar ƙungiyar saboda fargabar cewa ayyukansu na iya zama babbar barazana ga tsaron mazauna yankin.

Kungiyar 'yan ta'adda ta bulla a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mambobin kungiyar na yin tsubbu

A cewar mazauna yankin, mambobin ƙungiyar ana alaƙanta su da ayyukan tsubbu, damfara, da kuma ɗaukar matasa marasa madogara zuwa cikin sahunsu.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana bisa sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce ƙungiyar ta shafe kusan shekaru biyu tana aiki a jihar ba tare da janyo hankalin hukumomin tsaro ba.

Tsohon shugaban APC ya mutu a tsare

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani tsohon shugaban jam'iyyar APC a jihar Kebbi, ya rasa ransa a hannun 'yan bindigan da suka tsare shi a daji.

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Koko/Besse a Kebbi, Alhaji Muhammadu Besse, ya rasu yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga.

'Yan bindiga dai sun yi garkuwa da Alhaji Muhammadu Besse ne tare da wani abokinsa, kuma su duka biyun sun rasa rayukansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng