An Kama Mota Cike da Takalma irin na Sojoji Ta Nufi Dajin Zamfara
- Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin Operation Fansan Yamma sun kama wanda ake zargi da shirin kai wa 'yan ta'adda kaya a Zamfara
- Sojojin Najeriya sun yi nasarar kwato takalma irin na sojoji guda 150 da wasu kayayyakin da dakaru ke aiki da su da kuma da na'urori a wajensu
- Bayanai sun nuna cewa ana ci gaba da bincike game da mutanen, yayin da sojoji suka bukaci jama'a su rika bayar da sahihan bayanai ga jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Sojojin rundunar Operation Fansan Yamma sun kama wani mutum da ake zargi da kai wa 'yan ta'adda kayan aiki a Zamafara.
Dakarun kasar sun yi nasarar kwato tarin kayayyakin aikin soja a yayin wani bincike na yau da kullum da aka gudanar a kan titin Sokoto zuwa Gusau a jihar Zamfara.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai game da yadda aka kama wanda ake zargin ne a wani sako da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.
Yadda aka kama mutumin
Majiyoyi sun shaida cewa an tare wanda ake zargin ne a ranar 24 ga Yunin 2026 yayin da yake tuka mota kirar Honda Civic dauke da kayayyakin da suka shafi aikin soja da na'urorin lantarki.
An bayyana cewa ana kyautata zaton an nufi kai wa kungiyoyin 'yan ta'adda da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma kayayyakin da aka kaman ne.
An kama takalman sojoji
Kayayyakin da aka samu a cikin motar sun hada da takalma irin na sojoji guda 150, wukake guda uku, na'urorin wutar lantarki guda uku, kwalbar borkonon tsohuwa guda daya, hular soja guda daya da kuma bel guda daya.
Sojojin sun kuma kwace wayoyin Android guda biyu, iPad guda daya da agogon hannu na zamani guda daya, wadanda ake kyautata zaton za su taimaka wajen ci gaba da bincike.
An tsare wanda ake zargin domin ci gaba da yi masa tambayoyi, yayin da ake tantance kayayyakin da aka kwato a matsayin wani bangare na kokarin dakile hanyoyin samar da kayayyaki da tallafawa 'yan ta'adda a yankin.

Source: Facebook
An yabawa sojojin Najeriya
Mahukuntan soja sun ce kamen ya nuna irin jajircewar rundunar Operation Fansan Yamma wajen hana safarar kayayyaki da kayan aiki da ake amfani da su wajen ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso Yamma.
Sun kuma bukaci al'umma da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin tallafa wa ayyukan yaki da ta'addanci da ake ci gaba da gudanarwa.
An kama kayan sojoji a Legas
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Legas ta kama wasu mutane uku dauke da kayan sojoji.
Rahotanni sun nuna cewa a kama mutanen ne yayin da suka shiga Legas a cikin wata babbar mota suna shirin wucewa Kudu maso Gabas.
An bayyana cewa daga cikin abubuwan da aka samu a cikin motar akwai tarin kayan sojoji da abubuwan da ake zargi miyagun kwayoyi ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

