Na saci mota ne don na hada kudin aure – Mai laifi
Rundunar yan sandan jihar Niger sun gurfanar da wani Yusuf Duguri mai shekaru 26 da Abubakar Adamu mai shekaru 45 dukkaninsu daga yankin Gedi-Gedi na Zaria Road, jihar Kano, bisa zargin satar mota.
A cewar yan sanda, masu laifin sun tunkari Umar Abdulazeez na Bagdad Motors, Bauchi da yaudarar cea zasu siya motarsa Honda Accord mai dauke da lamba, YAB734 AR.
An tattaro cewa mai sayar da motan ya basu makulin motar domin su dana kawai sai Duguri da Adamu suka harce da motar.
An rahoto cewa masu laifin sun yiwa mutumin asiri ne.
KU KARANTA KUMA: An kama wani Mahauci da ya kware wurin yanka Kare yana gasawa ya sayarma da mutane
An tattaro cewa an kama su ne a yayinda suke tattaunawa don siyar da motar satan a Suleja.
Duguri ya fadama majiyarmu cewa sun aikata hakan ne bisa ga bayani da suka samu daga wani day a amfana daga satan.
“Muna sata a dukkanin jihohin arewa ya danganta da yanayin wajen da motar yake. A zaran mai basu bayani ya kiramu sannan ya fada mana inda motar yake, sai muyi gaggawan zuwa mu wanki mai motar,” yayi bayani.
“Na so na daina satar mota amma lokacin da matata da mahaifina suka mutu a rana daya, ya zama dole na nemi kudi na sake aure saboda b azan iya zama ni kadai ba. Gaskiyar lamari, shirina shine na dazaran na samu isasshen kudi nayi aure zan daina sana’ar sata,” cewar shi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng