Almubazaranci a yayin aure ke haddasa mutuwar aure - Sultan

Almubazaranci a yayin aure ke haddasa mutuwar aure - Sultan

Sultan na Skoto, Muhammad Sa’ad Abubakar, yace almubazaranci yayin bikin aure ke haddasa mace-macen aure.

Sultan na Magana ne a wani taron malaman Musulunc da hukumar Zakka ta jihar Sokoto ta shirya a jihar.

Yace: “Malaman mu na bukatar sanar da mutane akan illar yin bukukuwan aure ba bisa ka’ida ba kuma almubazaranci a yayin bikin. Wannan abu baya haifar da komai face rudani da mace-macen aure marasa ma’ana wanda ya zamo abun damuwa da ake tattaunawa a tsakanin jama’a.”

Almubazaranci a yayin aure ke haddasa mutuwar aure - Sultan

Almubazaranci a yayin aure ke haddasa mutuwar aure - Sultan

Sultan ya bukaci malamai da su ji tsoron Allah a koda yaushe a cikin ayyukansu da yadda suke tafiyar da abubuwa, cewa wannan zai kawo ci gaba a halayyan jama’a.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Karya ne ba’a kara wa’adin hutun shugaba Buhari ba – Fadar shugaban kasa

Ya kara da cewa akwai bukatar a dunga taimakawa marasa karfi a koda yaushe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel