Yanzu Yanzu: Murna ya koma ciki yayinda alkali ya umurci a kama shugaban INEC Yakubu kwana daya bayan umurnin kotun daukaka kara
Babban kotun tarayya dake Abuja tace lallai sai sufeto janar na yan sanda ya kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu sannan ya gabatar da shi a kotu a ranar 16 ga watan Agusta.
Justis Stephen Pam ne ya bayar da umurnin bayan rashin hallaran tawagar lauyoyin Yakubu a kotu sannan kuma babu wani bayani kan dalilin rashin hallararsu.
“A farkon zaman, lauyan mai kara, Kanayo Okafor ya sanar da kotu cewa kotun daukaka kara a ranar Litinin ta bukaci kotu da ta janye lamarin.
“Lauyan dake kare wanda ake kara bai halarci kotu ba sannan kuma babu dalilin da aka bayar akan rashin hallaransu."
Don haka kotun tace tana nan akan bakanta na kama Shugaban INEC din.
Don haka yayinda alkali ke yanke hukuncinsa, lauya daga tawagar masu kare Yakubu ya shigo kotun sannan yayi yunkurin jan hankalin alkalin zuwa gare shi.
Sai dai hakan bai yiwuwa ba yayinda Justis Pam y adage karar juwa ranar 16 ga watan Agusta don ci gaba da shari’a.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta bayyana cewa lauyan yayi latti ne saboda ya je kotun daukaka kasar yana kokarin karban takardan da zai gabatarwa kotun, amma takardan bai kammalu ba.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Bafarawa ya ziyarci IBB a Minna
Kotun tace lallai bata da masaniya akan wannan umurni domin ba’a sanar da ita akan hakan ba sannan kuma babu wani rahoto akai, don haka tana bukatar takarda da zai nuna cewa akwai wannan umurni ba wai kalamun baki ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng