Ban san yadda aka yi rayuwata ta susuce ba – Zainab Indomie

Ban san yadda aka yi rayuwata ta susuce ba – Zainab Indomie

Shahararriyar jarumar da tauraronta ya daina haskawa a Kannywood, Zainab Abdullahi wacce aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa ba ta san yadda aka yi rayuwar jarumtarta ta susuce ba duk da daukakar da ta samu a masana’antar fina-finan Hausa a baya.

Jarumar ta ce ta samu daukaka tun tana karama, amma saboda kaddara ba ta san abin da ya faru ba yanzu ta rasa komai.

Ban san yadda aka yi rayuwata ta susuce ba – Zainab Indomie

Ban san yadda aka yi rayuwata ta susuce ba – Zainab Indomie

Zainab ta nemi yafiyar Allah akan jarabtar da take fuskanta, inda tace idan laifi ta aikata toh rabbi yayi mata rangwame, sannan kuma tace idan har da hannun wani a cikin lamarinta toh tana rokon Allah ya yafe masa.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar arewa na so Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa, sun bukaci Oshiomhole ya tabbatar da tsige Saraki

Daga karshe ta roki Allah ya sanya ta da sauran jama’a a kan hanya madaidaiciya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Online view pixel