Ba na adawa da amfani da katin zabe da na’urar tantance katin zabe - Buhari

Ba na adawa da amfani da katin zabe da na’urar tantance katin zabe - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ga laifin wani rahoton dake cewa shi yana adawa da amfani da katin zabe da kuma na’urar tantance katin zaben a zabe mai zuwa.

Buhari a wata sanarwa a jiya ta hannun babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu yace zarge-zargen cewa yaki sanya hannu a dokar da aka gabatar masa saboda yana adawa da amfani da na’urar tantance katin zabe ba gaskiya bane kuma baida tushe.

“Shugaba Buharu bai taba nuna adawa ga amfani da na’urar tantance katin zabe ba a zabukan Najeriya.

Ba na adawa da amfani da katin zabe da na’urar tantance katin zabe - Buhari
Ba na adawa da amfani da katin zabe da na’urar tantance katin zabe - Buhari

“Sabanin haka a koda yashe yana nuna ga amfani da katin zabe da na’urar tantance katin zabe a zabukan Najeriya, duba ga irin rawar ganin da katiun zaben da na’urar tantance katin suka taka wajen kawo shi ga matsayin da yake kai a zaben da ya gabata. Kuma ya sha fadin haka da kuma yabama hakan,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudi: Honarabul Abdulmumin Jibrin ya yabawa Gwamnatin El-Rufai

Yace akan dokar zabe da aka gyara wanda majalisar dokokin kasar ta gabatar a ranar 2 ga watan Agusta bai shiga hannun shugaban kasa sai a ranar 3 ga watan Agusta.

Kuma yana da kwanaki 30 daga ranar da ya karbi takardan don haka yana shawarwari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng