Zaben 2027: An Fara Hasashen Siyasa bayan Obasanjo Ya Gana da Kwankwaso a Kano

Zaben 2027: An Fara Hasashen Siyasa bayan Obasanjo Ya Gana da Kwankwaso a Kano

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ta musamman ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a jihar Kano
  • Kwankwaso tare da dan takarar gwamna na NDC a Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, sun tarbi Obasanjo yayin da suka gaisa cikin yanayi na mutuntawa
  • Mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yada labarai ya ce an yi tattaunawa mai kyau, amma bai bayyana cikakken abin da shugabannin suka tattauna ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya kai ziyara na musamman ga Rabiu Musa Kwankwaso.

'Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC ya karbi bakuncin Olusegun Obasanjo a gidansa da ke titin Miller a Kano.

Obasanjo ya gana da Kwankwaso a Kano
Olusegun Obasanjo yayin ganawa da Rabiu Kwankwaso da Abdulsalam Aminu Gwarzo a Kano. Hoto: Hon. Saifullah Hassan.
Source: Facebook

Mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yada labarai, Saifullahi Hassan, ya tabbatar da faruwar ziyarar cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa a Facebook.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi: Tsohon sanata kuma jigonta ya yi bankwana da duniya

Obasanjo ya gana da Kwankwaso a Kano

Kwankwaso tare da dan takarar gwamna na NDC a Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo ne suka tarbi Obasanjo.

Ya bayyana cewa ziyarar ta bai wa shugabannin damar gaisawa da tattaunawa cikin yanayi na sada zumunci, amma bai bayyana cikakken bayanin tattaunawar ba.

Kwankwaso ya taba rike mukamin ministan tsaro a wa’adi na biyu na gwamnatin Obasanjo tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007, inda suka yi aiki tare a matakin tarayya.

Tun bayan wannan lokaci ne aka ce dangantaka mai kyau ta ci gaba da kasancewa tsakanin Kwankwaso da Obasanjo, lamarin da ya sa suke ci gaba da mu’amala.

Daga bisani, Saifullah Hassan ya tabbatar a Facebook cewa Obasanjo, Kwankwaso da manyan mutane daga fadin Najeriya sun isa fadar Sarki Muhammadu Sanusi II domin bikin nadin sarauta.

Ya ce:

"Mai Girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, ya isa Fadar Mai Martaba Sarkin Kano domin halartar bikin naɗa rawanin Abubakar Balarabe Mahmoud, OON, SAN, a matsayin Garkuwan Kano."

Kara karanta wannan

Kano ta yi zarra, ta fi dukkan jihohin Najeriya sababbin masu rijistar katin zaɓe

Ana hasashen siyasa bayan ganawar Obasanjo da Kwankwaso
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Peter Obi, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: @PeterObi.
Source: Twitter

Alalar da ke tsakanin Obi da Obasanjo

'Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, shi ma na daga cikin makusantan Obasanjo kuma yana da kyakkyawar alaka da tsohon shugaban kasar.

Obasanjo ya goyi bayan Obi a zaben shekarar 2023, yayin da rahotanni ke cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen hada kawancen siyasa tsakanin Obi da Rabiu Kwankwaso domin zaben 2027.

Sai dai sanarwar da ta tabbatar da ziyarar ba ta bayyana ko batun siyasar 2027 ko wasu muhimman al’amuran kasa sun kasance cikin abubuwan da aka tattauna ba.

Ziyarar ta jawo hankalin masu bibiyar harkokin siyasa, musamman saboda matsayi da tasirin da Obasanjo da Kwankwaso ke da shi a siyasar Najeriya.

Kwankwaso ya yi barazana ga Fasto Ayodele

Mun ba ku labarin cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi barazanar shigar da kara kan.

Kara karanta wannan

Zargin bata suna: Fasto Ayodele ya fayyace komai a martani ga barazanar Kwankwaso

Primate Elijah Ayodele Sanata Kwankwaso ya yi barazanar shigar da karar ne kan malamin addinin saboda zargin bata masu suna da kimarsa ta siyasa.

Madugun na Kwankwasiyya ya ce Primate Ayodele ya yi kalamai wadanda suke na cin mutunci ne a gare shi da kuma kimarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.