Hodijan! Jakadan Najeriya ya bar APC saboda sabani da gwamnansa

Hodijan! Jakadan Najeriya ya bar APC saboda sabani da gwamnansa

Ambasada James Barka, tsohon mukaddashin gwamnan jihar Adamawa kuma makusancin Gwamna Umaru Jibrilla ya bar jam’iyyar APC mai mulki.

Barka yayinda yake sanar da ficewarsa daga APC ya kuma warware kullinsa daa gwamnan jihar bisa zargin rashin mutunci.

Ba’a san ko tsohon jakadan Najeriyan a kasar Malaysia wanda ya kasance mamba na kwamitin shugaban kasa akan shirin arewa maso gabas yayi murabus ba kafin ya sauya sheka zuwa PDP a ranar Juma’a.

Hodijan! Jakadan Najeriya ya bar APC saboda sabani da gwamnansa
Hodijan! Jakadan Najeriya ya bar APC saboda sabani da gwamnansa
Asali: Depositphotos

Da yake bayyana dalilinsa na barin jam’iyyar, tsohon mukaddashin gwamnan na jihar Adamawa yayi korafin cewa jam’iyyar ta watsar da shi da kuma rashin kirkin gwamnan.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai, masu zanga-zanga sun kunyata Kwankwaso sunyi masa ihun ‘Sai Buhari’ a filin jirgi (bidiyo)

Yace “Ya kamata mutane su kasance masu aminci. Idan suka ce eh toh eh ne.

“Idan kace shugaba mu hadu gobe da misalin karfe 11 na safe, toh ya tabbata hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng