Shawarar da Tsohon Shugaban Kungiyar CAN Ya ba Tinubu kan Sake Takara a 2027
- Fasto Ayo Oritsejafor ya ce Shugaba Bola Tinubu ya gaza wajen jagoranci, don haka bai kamata ya sake neman mulki a 2027 ba
- Oritsejafor ya ce gwamnatin Tinubu ta jefa ‘yan Najeriya cikin ƙarin matsaloli, yana mai ba shugabannin kasar shawara
- Tsohon shugaban CAN ya kuma soki zaɓuɓɓuka a Najeriya, yana mai cewa sau da yawa sakamakon ba ya nuna ainihin ra’ayin mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), Ayo Oritsejafor, ya yi magana game da salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Oritsejafor ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ka da ya sake neman takara a zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.

Source: Twitter
Da yake magana a shirin Politics Today na Channels Television, ya ce gwamnatin Tinubu ta yi wa Najeriya illa fiye da alherin da ta kawo.
Fasto Oritsejafor ya koka da mulkin Tinubu
Oritsejafor ya bayyana cewa salon mulkin Tinubu a cikin shekaru uku da suka gabata ya gaza biyan bukatun ‘yan Najeriya.
Malamin ya ce ya dace shugaban ya nemo ƙwararru masu cancanta da za su karɓi ragamar mulki domin kawo sauƙi ga ‘yan ƙasa.
A cewarsa, Najeriya na ci gaba da komawa baya maimakon ta samu ci gaba, yayin da matsaloli ke ƙaruwa maimakon a warware su.
Ya ce:
“Lokacin da ka kalli halin da ƙasar nan take ciki yanzu, za ka ga muna komawa baya maimakon ci gaba.”
Oritsejafor ya ce ba zai fito fili ya ce Tinubu ya yi murabus ba, amma ya kamata ya amince idan ya kasa magance matsalolin ƙasar.
Ya ƙara da cewa talakawan Najeriya sun rasa kwarin guiwa, duk da cewa ana ta maganar manufofin “Renewed Hope” na gwamnati.
A cewarsa, Shugaba Tinubu bai kamata ya yi tunanin dawowa wa’adin mulki na biyu domin ci gaba da abin da ya kira rikicin shugabanci ba.

Source: Facebook
Kura-kuran hukumar INEC da faston ya gano
Oritsejafor ya ce tsarin zaɓen daga matakin shugabannin hukumar INEC zuwa ƙananan hukumomi yana da kura-kurai masu yawa.
Ya ce ƙuri’ar talakan Najeriya ba ta da tasiri saboda wasu sun riga sun tsara wanda zai yi nasara kafin zaɓe.
Malamin ya ce idan ya samu ganawa da Tinubu, zai gaya masa cewa ya gaza kuma bai yi abin da ake tsammani ba.
Ya buƙace shi da ya janye daga takara ko kuma ya nemo mutanen da ke da ikon kawo sauyi ga Najeriya.
Oritsejafor ya ƙara da cewa coci za ta ci gaba da faɗin gaskiya ga masu mulki domin kare muradun jama’a.
Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus
Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben badi, Peter Obi, ya yi kira da babbar murya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Peter Obi ya bukaci shugaban kasar da ya yi murabus saboda gaza cika dumbin alkawuran da ya daukarwa 'yan Najeriya.
Ya bukaci hakan ne bayan ganin yadda Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya yi murabus daga mukaminsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

