Peter Obi Ya Kai Karar Jigon ADC Kotu, Ya Nemi N8bn kan Zargin Bata Suna
- 'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya shigar da kara a gaban kotu kan jigo a ADC, Kenneth Okonkwo
- Peter Obi ya shigar da karar ne bayan ya zargi tsohon mai magana da yawun bakin nasa da bata masa suna ta hanyar yin waau kalamai
- Dan takarar shugaban kasar ya nemi abubuwa da dama a cikin karar, ciki har da Naira biliyan 8 a matsayin diyya daga wajen Okonkwo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya shigar da kara kan tsohon mai magana da yawun bakinsa kuma tsigo a ADC, Kenneth Okonkwo.
Peter Obi ya shigar da karar ne inda yake neman Naira biliyan 8 daga wajen Kenneth Okonkwo, kan zargin ɓata masa suna.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta kawo rahoton cewa Peter Obi ya shigar da ƙarar ne a babbar kotun jihar Anambra da ke birnin Onitsa a ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana a Arewa
Okonkwo ya yi zargin cewa Obi ya damfari masu neman takarar kujerun Majalisar Wakilai da kuɗi Naira miliyan 10 kowannensu, sannan ya ci gaba da rubuta jerin sunayen 'yan takara na mazaɓun tarayya daban-daban a shiyar Kudu maso Gabas.
Wadanne bukatu Peter Obi ya nema?
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa a cikin kwafin takardar sammacin kotu da aka fitar, Peter Obi ya bayyana abubuwan da yake son samu daga wajen Kenneth Okonkwo.
Sammacin, mai kwanan wata 25 ga Yunin 2026, lauyan Peter Obi mai suna Alex Ejesieme (SAN) ne ya fitar da shi.
Kotun ta amince da sammacin, sannan ta ba da ikon isar da shi ga Mista Okonkwo “a wajen Jihar Anambra kuma a cikin Jihar Enugu” inda wanda ake ƙarar yake zaune.
A cikin sammacin, an bayyana Obi a matsayin mai ƙara yayin da aka bayyana Okonkwo a matsayin wanda ake kara shi kaɗai a cikin ƙarar mai lamba 0/229/26.
Obi, a cikin bayanansa, ya toge kan cewa zargin da Mista Okonkwo ya yi masa a shirin talabijin da kuma martanin da ya mayar wa wasiƙarsa ta gargaɗi kafin shari'a, wanda ya yaɗa a shafukansa na sada zumunta, sun kasance “na ƙarya, na ƙeta, marasa tushe kuma na ɓata suna” gare shi.
Peter Obi ya nemi diyya daga wajen Okonkwo
'Ɗan takarar na NDC ya buƙaci Okonkwo da ya biya shi Naira biliyan 5 a matsayin diyya saboda bata “mutuncinsa, halayensa, amincinsa, kimarsa a idon al'umma, matsayinsa na siyasa da kuma kyakkyawar niyyarsa sakamakon wallafe-wallafen ɓata suna na Mista Okonkwo.”
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kuma buƙaci Okonkwo ya biya shi Naira biliyan 2 a matsayin diyya saboda “yanayi, faɗi, dagewa, da kuma maimaita wallafe-wallafen,” ciki har da wallafe-wallafen da Okonkwo ya yi bayan ya karɓi wasiƙar gargaɗi da ke neman janye kalamansa da ba da haƙuri.
Haka kuma ya buƙaci biyan Naira biliyan 1 daga gurin Okonkwo a matsayin diyya saboda “maimaitawa da gangan da kuma ƙara faɗaɗa zargin” bayan ya karɓi wasiƙar gargaɗi ta neman janye kalamansa da ba da haƙuri.

Source: Twitter
Peter Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya bar karagar mulki..

Kara karanta wannan
Zargin bata suna: Kwankwaso ya yi barazanar kai malamin addini kotu, zai nemi N10bn
Peter Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus ne domin ya yi koyi da Firaministan Burtaniya, Keir Starmer, wanda ya sauka daga mukaminsa.
Obi ya ce ya kamata shugaban Najeriyan ya yi murabus domin ya gaza cika alkawura da dama da ya daukarwa 'yan kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
