An sanyawa wani kyakyawan yaro a gidan marayu sunan shugaba Buhari

An sanyawa wani kyakyawan yaro a gidan marayu sunan shugaba Buhari

Shugaban kasar Najeriya na iya kasancewa da tarin makiya da mutanen dake sauraron ganin an tsige shi daga fadar shugaban kasa amma duk da haka yana da mabiya da yawa da suke ganinsa a matsayin abu mafi inganci day a taba samun Najeriya.

Ba sabon abu bane mutane su sanya wa yaransu sunayen manyan shugabanni da kuma mutanen da suka kafa tarihi ta hanyar kawo chanji a duniya.

Irin haka ne ya faru da wani kyakyawan yaro a gidan marayu dake Borno. An sanyawa kyakyawan sadaukin sunan Buhari.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ba zamu iya dawowa majalisa ba yanzu – Saraki, Dogara

A cewar wata mai amfani da shafin Facebook mai suna Fati Abubakar wacce ta wallafa labarin yaron tace an sanyawa yaron sunan shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

An sanyawa wani kyakyawan yaro a gidan marayu sunan shugaba Buhari

An sanyawa wani kyakyawan yaro a gidan marayu sunan shugaba Buhari

Abu yayi kyau!

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel