Mamayar majalisa: Osinbajo ya ceci Najeriya daga tozarci - Tinubu
Uban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata ya yabama mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo kan sanya baki da yayi a lamarin mamayar da aka kai majalisar dokokin kasar.
Tinubu ya yabama Osinbajo ne a yayinda yake jawabi ga mambobin jam’iyyar sakatariyar jiha na jam’iyyar.
Yace martanin Osinbajo na dakatar da darakta Janar na hukumar yan sandan farin kaya (DSS) ya taimaka wajen kwantar da tarzoman da ya tashi sakamakon mamayar.
Jigon APC ya bayyana mamayar a matsayin barazana ga damokradiya, cea Osinbajo ya taimaki kasar daga tozarci ta hanyar sanya baki.
KU KARANTA KUMA: Babban sakataren gwamnati yayi hasashen nasarar Buhari a zaben 2019
Tinubu yace APC na matukar mutunta damokradiyar kasar kuma zata ci gaba da yin hakan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng