APC Na Shirin Sauya Dan Takararta na Gwamna a Adamawa? Jam'iyyar Ta Yi Bayani

APC Na Shirin Sauya Dan Takararta na Gwamna a Adamawa? Jam'iyyar Ta Yi Bayani

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa ta yi magana kan batun cewa tana shirin canza dan takararta na gwamna a zaben 2027
  • Sakataren yada labarai na jam'iyyar APC ya bayyana cewa sun gamsu da zabin da aka yi na Tijjani Galadima a matsayin dan takarar gwamna
  • Ya bayyana cewa akwai shirin da ake yi domin ganin an kara farin jinin dan takarar gwamnan gabanin babban zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa ta yi martanin kan batun cewa tana duba yiwuwar sauya dan takararta na gwamna a zaben 2027.

APC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa tana duba yuwuwar canza Alhaji Tijjani Galadima a matsayin ɗan takararta na gwamna gabanin zaɓen shekarar 2027.

APC ta ce tana da kwarin gwiwa kan Galadima
Dan takarar gwamnan APC a Kebbi, Alhaji Tijjani Galadima, na jawabi a wajen taro Hoto: Ahmed Tijjani Galadima Political Movement
Source: Facebook

Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar APC a jihar Adamawa, Dogo Victor, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar The Punch ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

"Ba a bayar da mulki"; Shawarar da Wike ya ba Pantami da sauran 'yan takarar PDP

Me APC ta ce kan batun sauya Galadima?

Dogo Victor ya bayyana iƙirarin a matsayin na ƙarya, inda ya jaddada cewa babu wani shiri na sauya Galadima.

“Muna jin dukkan waɗannan zargi kan shirye-shiryen canza Galadima; babu wani abu mai kama da haka. Shi ne ɗan takarar gwamna na shekarar 2027 na jam'iyya mai mulki ta APC a jihar Adamawa."
"Ka yarda da wannan magana daga gare ni a matsayina na mai magana da yawun jam'iyyar a jihar Adamawa."

- Dogo Victor

An nuna damuwa kan farin jinin Galadima

An nuna damuwa a wasu ɓangarori na jam'iyyar game da abin da aka bayyana da rashin kasancewar Galadima a jihar akai-akai da kuma ganin cewa ba shi kusa da jama'a.

Yayin da yake mayar da martani kan hakan, Dogo Victor ya ce ana yin ƙoƙari domin gabatar da Galadima ga ƙarin mambobin jam'iyya da kuma mutanen jihar.

“Idan ka lura a kwanan nan, duk inda Gwamna Ahmadu Fintiri zai tafi, yana bin gwamnan; wannan wata dabara ce da aka yi amfani da ita domin gabatar da shi ga mutane, kafin a fara kamfen ɗin zaɓe na gaske."

Kara karanta wannan

Babbar mota ta burma kan 'yan APC suna tafiya kamfen, an samu asarar rai

- Dogo Victor

APC ta ce ta gamsu da Galadima

Dogo Victor ya kuma yi watsi da batun cewa ɗan kasuwa Abdulrahman Haske zai iya canzar Galadima, inda ya nuna cewa jam'iyyar tana da kwarin gwiwa ga zaɓin da ta yi a yanzu.

To sai dai kuma, wani mamba a kwamitin gudanarwa na APC na jihar, wanda ya yi magana cikin sharadin sakaya sunansa, ya nuna damuwa game da shaharar Galadima a gurin masu zaɓe.

APC ta gamsu da zabin Galadima
Dan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam'iyyar APC, Alhaji Tijjani Galadima Hoto: Ahmed Tijjani Galadima Political Movement
Source: Facebook

Jami'in jam'iyyar ya yi zargin cewa da karfi aka ba Galadima takara, kuma ya yi gargaɗin cewa APC tana iya fuskantar ƙalubale idan ta gaza gina babban goyon baya gare shi gabanin zaɓen.

Duk da hakan, Dogo Victor ya nace kan cewa Galadima ya kasance ɗan takarar da jam'iyyar ta fi so, kuma ba ya da wani cikas a cikin APC gabanin zaben gwamnan.

APC ta dakatar da shugabanta a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi ta dakatar da shugabanta na jihar da na karamar hukumar Zuru.

Kara karanta wannan

"Ba makamin azabatarwa ba ne"; Atiku ya nuna damuwa kan sharuddan belin El Rufai

Jam’iyyar APC ta ce matakin ya biyo bayan damuwa da aka samu kan yadda ta gudanar da ayyukanta a zaben cike gurbin mazabar Zuru.

A cewar sanarwar da jam’iyyar ta fitar, an zargi shugabannin da aka dakatar da nuna rashin himma wajen gudanar da ayyukan jam’iyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng