Cire Saraki ba zai rage farashin shinkafa zuwa N7,000 ba – Fayose

Cire Saraki ba zai rage farashin shinkafa zuwa N7,000 ba – Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a ranar Laraba yace yana mamakin ko tsige Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa zai rage farashin buhun shinkafa zuwa N7,000 a kasuwan in Najeriya.

Fayose na martani ne akan kiraye-kiraye da ake yi kan tsige Saraki tun bayan da ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP.

Ya wallafa hakan ne a shafinsa na twitter wato @ayofayose.

A halin da ake ciki, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya tirje akan cewa lallai sai shugaban majalisar dattawa, ya sauka daga matsayinsa ko kuma su tsige shi.

KU KARANTA KUMA: 2019: Manyan yan takarar kujerar shugaban kasa 4 da suka ziyarci Obasanjo kwanan nan

Oshiomhole yace ba zai yiwu Saraki ya yi jagoranci ba alhalin APC ce ke da mafi rinjayen sanatoci a majalisar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel