Gwamnatin Tinubu ta Jero Mutane da Kamfanoni 9 Masu Tallafawa 'Yan ta'adda
- Gwamnatin tarayya ta sanya mutane shida da kamfanonin canjin kudi uku cikin wadanda aka sa wa takunkumi bisa zargin hannu a harkokin tallafa wa ta'addanci
- Matakin ya biyo bayan sanya takunkumi da Amurka ta yi wa Muktar Muhammad Adamu da wasu kamfanoni da ke da alaka da shi, bisa zargin hulɗar da ISWAP
- Hukumomi sun umurci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su gaggauta daskarar da duk wasu kadarorin wadanda abin ya shafa nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta sanar da sanya wa mutane shida da kamfanoni uku takunkumi saboda zargin hannu a ayyukan tallafa wa ta'addanci a Najeriya.
Sakatariyar kwamitin takunkumin Najeriya, Beatrice Jedy-Agba, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa an amince da sabunta jerin sunayen.

Source: Facebook
Sunayen wadanda ake zargi
Premium Times ta rahoto cewa an wallafa sunayen mutanen ne a watan Yunin 2026 bayan gudanar da bincike da tantance bayanan sirri game da waɗanda ake zargin.
Sunayen mutanen da gwamnatin Najeriya ta sanya cikin jerin sun hada da:
- Ibrahim Yakubu Ogirima
- Muktar Muhammad Adamu
- Adamu Chiroma
- Ibrahim Abubakar
- Abdullahi Umar Usman
- Babangida Muhammed Adamu Hammajam
Vanguard ta wallafa cewa kamfanonin da aka sanya wa takunkumin kuwa sun hada da:
- Abbal Bako & Sons Bureau De Change Limited
- Generation Currency BDC Limited
- Nine to Nine BDC Limited
Dalilin sanya takunkumi da aka yi
Jedy-Agba ta ce sanya takunkumin ya biyo bayan tattara bayanan sirri mai zurfi, binciken hada-hadar kudi da kuma tantancewa tsakanin hukumomi.
Ta kara da cewa bayanan sun tabbatar da cewa akwai dalilai masu karfi na zargin mutanen da kamfanonin da abin ya shafa da bayar da gudummawa ko taimakawa ayyukan ta'addanci.

Source: Twitter
Kiran Najeriya ga bankuna
Najeriya ta bukaci bankuna da sauran waɗanda abin ya shafa su gaggauta aiwatar da takunkumin ta hanyar daskarar da kadarori da kuma kai rahoton duk wata mu'amala da ake zargi ga hukumomin.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnatin tarayya ta sake jaddada umarninta ga dukkan cibiyoyin hada-hadar kudi da sauran sana'o'i da kasuwancin da doka ta tanada da su ci gaba da bin dukkan ka'idojin takunkumi, ciki har da daskarar da kadarori, gabatar da rahotannin mu'amalolin da ake zargi, da kuma sanar da hukumomin da suka dace duk wasu bayanan da suka yi daidai da jerin sunayen."
Gwamnatin ta kuma sake tabbatar da kudurinta na toshe hanyoyin samun kudi da kungiyoyin 'yan ta'ada ke amfani da su tare da kara kaimi wajen yaki da tallafa wa ayyukan ta'addanci ta fuskar kudi.
Amurka ta zargi dan Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Amurka ta sanya dan Najeriya cikin wadanda ake zargi da tallafawa kungiyar 'yan ta'addan ISWAP.
Amurka ta ce, wanda ake zargin, Muktar Muhammad Adamu ya yi mu'amalar kudi da ISWAP kuma yana zaune a jihar Legas da ke Kudancin kasar.
Hakazalika, Amurka ta zargi wasu kamfanonin canjin kudi uku a Najeriya da ke jihohin Kano da Legas da wasu 'yan kasashen Faransa da Syria.
Asali: Legit.ng


