Dan Majalisar Amurka Ya Fadi Kokarin da Ya Yi don Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

Dan Majalisar Amurka Ya Fadi Kokarin da Ya Yi don Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

  • Dan majalisar Amurka da ke magana kan tsaron Najeriya, Riley Moore ya yaba da amincewar majalisar dattawa da kudirin kafa 'yan sandan jihohi
  • Ya ce matakin zai taimaka wa jihohin kasar nan wajen magance matsalolin tsaro da kare al'umma yadda ya kamata, musamman Kiristoci
  • A bayanan da ya yi, Moore ya yabawa shugaba Bola AhmedTinubu bisa goyon bayan kudirin da ya yi domin tabbatar da zaman lafiya a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya yi maraba da amincewar majalisar dattawan Najeriya da kudirin dokar kafa rundunar 'yan sandan jihohi.

Ya yi magana yana mai bayyana matakin a matsayin wani gagarumin ci gaba wajen inganta tsaro da kare al'ummomin da ke cikin hadari.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Tinubu kan batun kafa yan sandan jihohi a Najeriya

Riley Moore da ke Amurka
Dan majalisar Amurka, Riley Moore. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Legit Hausa ta gano cewa dan majalisar ya yi magana game da kafa 'yan sandan jihohi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Maganar dan majalisar Amurka

Moore, wanda a baya ya sha bayyana damuwarsa kan tashe-tashen hankula da suka shafi al'ummomin Kiristoci a wasu sassan Najeriya, ya yi magana bayan majalisa ta amince da kafa 'yan sandan jihohi.

Ya ce gyaran tsarin da ake son yi zai bai wa gwamnatocin jihohi damar mayar da martani yadda ya kamata ga matsalolin tsaro da ke faruwa a yankunansu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, dan majalisar ya ce ya dade yana goyon bayan ra'ayin kafa 'yan sandan jihohi, a fili da kuma a sirrance, tun bayan da ya fara bibiyar rahotannin hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya.

Punch ta rahoto ya ce:

"Ina farin cikin ganin Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin kafa rundunar 'yan sanda a matakin jihohi, wani gyara da na dade ina kira a aiwatar da shi a bainar jama'a da kuma a sirrance tun lokacin da na fara bincike kan kashe-kashen Kiristoci a Najeriya,"

Kara karanta wannan

"Ba makamin azabatarwa ba ne"; Atiku ya nuna damuwa kan sharuddan belin El Rufai

In ji Moore.

Ya yi nuni da cewa rarraba ikon aikin 'yan sanda zuwa matakin jihohi zai rage yawan dogaro da shawarwarin da ake a matakin gwamnatin tarayya, tare da bai wa jihohi damar daukar nauyi kai tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'arsu.

Moore ya yabawa Tinubu

Moore ya kuma yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da ya bai wa wannan kudiri da kuma rawar da ya taka wajen ciyar da shi gaba.

"Ba zan iya bayyana muhimmancin wannan doka yadda ya kamata ba.
"Dokar za ta bai wa jihohi damar kare 'yan kasarsu tare da rage dogaro da masu yanke hukunci a Abuja, wanda hakan zai taimaka wajen kare Kiristocin da ake muzantawa da kuma magance matsalolin tsaro,"
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu yayin wani bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kara da cewa:

"Shugaba Tinubu ya cancanci yabo saboda kokarinsa na ciyar da kudirin gaba, amma yanzu ana bukatar akalla kashi biyu bisa uku na jihohin kasar su amince da shi kafin ya fara aiki,"

Kara karanta wannan

Malamar Islamiyya: Sufeton 'yan sanda ya dauki mataki kan DPO a Kaduna

Masu tallafawa ta'addanci a Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana sunayen mutanen da ake zargi na tallafawa 'yan ta'adda.

A wan rahoto da Najeriya ta fitar, an jeri sunayen mutane shida da wasu kamfanoni uku da ake zargin suna hada-hadar kudi da 'yan ISWAP.

Biyo bayan jero sunaye da kamfanonin, gwamnatin NAjeriya ta bukaci a kakaba masu takunkumi a bankuna da dukkan wuraren hada-hadar kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng