Dama Ta Samu: Gwamnan Sokoto Ya Yi Sababbin Nade Nade a Gwamnatinsa

Dama Ta Samu: Gwamnan Sokoto Ya Yi Sababbin Nade Nade a Gwamnatinsa

  • Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya zakulo wasu mutane domin shigar da su cikin gwamnati ta hanyar ba su mukaman da za a rika damawa da su
  • Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto ya nada masu bada shawara na musamman, manyan mataimaka na musamman da manyan sakatarori a gwamnatinsa
  • ​A cikin sanarwar da mai magana da yawun bakin gwamnan ya fitar, an bayyana cewa nade-naden za su fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto, tarayyar Najeriya - Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya yi sababbin nade-nade na wasu mukamai a gwamnatinsa.

Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da naɗin masu bada shawara na musamman, manyan mataimaka na musamman, manyan sakatarori da kuma mukaddashin babban sakatare.

Gwamnan Sokoto ya yi rabon mukamai
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto rike da abin magana Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Gwamna Ahmed ya yi nade-naden mukamai

Kara karanta wannan

"Kafin lokaci ya kure"; Yaron Gwamna Bala ya rubuta budaddiyar wasika ga mahaifinsa

An sanar da waɗannan naɗe-naɗe ne a cikin wata sanarwa da darakta janar na yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin shekarar 2026 a shafin yanar gizo na gwamnatin jihar.

Gwamnan ya nada masu ba da shawara na musamman guda shida, manyan mataimaka na musamman guda uku, manyan sakatarori guda huɗu, da kuma mukaddashin babban sakatare guda ɗaya.

An yi nade-nade a gwamnatin Sokoto

Bisa ga sanarwar, sababbin masu bada shawara na musamman da aka naɗa su ne Garba Muhammad S/Birni, Mukhtari Bello Abdurrahman, Shi’itu M. Bello, Alhaji Tukur Sanyinna, Alhaji Abdullahi Jabo, da kuma Mamman Aliyu Salisu.

Gwamnan ya kuma naɗa Jummai Bello Kware, Nana Mamman Nasarawa, da kuma Hon. Emmanuel Ekereke a matsayin manyan mataimaka na musamman.

Haka zalika, an naɗa Buhari Umar, Abdullahi B. Muhammad, Musa Muhammad, da Jibril Sa’adu a matsayin manyan sakatarori, yayin da aka sanya sunan Aliyu Magaji a matsayin mukaddashin babban sakatare.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa dukkan naɗe-naɗen za su su fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba.

Jerin sunayen waɗanda aka naɗa:

Kara karanta wannan

'Kashi 80 na matsalolin tsaro da suka addabi Sakkwato na da alaka da miyagun kwayoyi'

Masu bada shawara na musamman

Garba Muhammad S/Birni

Mukhtari Bello Abdulrahman

Shi’itu M. Bello

Alh. Tukur Sanyinna

Alh. Abdullahi Jabo

Mamman Aliyu Salisu

Manyan mataimaka na musamman

Jummai Bello Kware

Nana Mamman Nasarawa

Hon. Emmanuel Ekereke

Manyan sakatarori

Buhari Umar

Abdullahi B. Muhammad

Musa Muhammad

Jibril Sa’adu

Mukaddashin babban sakatare

Aliyu Magaji

Ahmed Aliyu ya yi nade-naden mukamai
Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto a dakin taro Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Gwamnan Sokoto ya yi maganar rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayyana alakar da ke tsakanin matsalar rashin tsaro da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa kusan kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaron da jihar ke fuskanta na da nasaba da shaye-shayen miyagun kwayoyi da ake yi.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa annobar shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar makomar matasa da ci gaban al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng