Yanzu Yanzu: Yan fashi sun kashe mutane 10, sannan sun sanyawa motar kwamanda wuta a harin bankunan Edo
An rahoto cewa akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hari da yan fashi suka kai Igarra, a karamar hukumar Akoko-Edo dake jihar Edo.
Kwamishinan yan sanda, Mista Johnson Kokumo ya tabbatar da al’amarin ga manema labarai.
Ko da yake ba a gama samun bayanai akan al’amarin ba a lokacin hada wannan rahoton. An tattaro cewa harin ya auku ne a yammacin ranar Alhamis.
An tattaro cewa yan bindigan sun kai mamaya garin ne a ranar Alhamis, yayinda suke yunkurin kai hari ga bankunan Unity da Keystone dake a yankin.
Daga farko sun addabi ofishin yan sanda dake kusa da harabar bankunan da niyyar fatattakar yan sanda.
Sunyi nasarar kashe wani dan sanda tare da wadansu mutane biyu da aka tsare a ofishin, yayinda yan fashin suka hallaka wassu mutane biyu a harabar ofishin yan sandan.
KU KARANTA KUMA: Da wuya idan ba nine zan fara zama shugaban kasa a yan Igbo ba - Okorocha
An gano cewa yan fashin sun kona motar sabon kwamandan da aka turo yankin.
Majiyarmu sun gano cewa yan fashin sun karasa bankunan ne inda suka kara kashe wassu mutane hudu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng