Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
John Agim, kakakin hedkwatar hukumar tsaro, ya fada ma mambobin kungiyar musulmai na ýan shi’a da su shirya sakamakon duk abun da suka yi ma sojoji. Mambbin kungiyar Shi’a sun kara da sojoji a wasu yankunan Abuja.
Yayinda zaben 2019 ke gabatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta haramta wa jami’an kasancewa mamba a kungiyoyin WhatsApp. Hukumar zaben ta aika da wata wasika ga dukkanin kwamishinonin zabe 37, inda take sanar masu hukuncin ta.
A wata sanarwa daga kakakin gwamnan jihar, Samuel Aruwan ya bayyana cewa jami’an tsaro sun dakatar da wani yunkuri na tayar da zaune tsaye a wuraren ibada da ke unguwannin Hayin Banki da kuma Kawo a cikin garin Kadunan.
A ranar Alhamis, 25 ga watan Oktoba, jarumin Kannywood, Lawan Ahmed ya yi bikin cikarsa shekara 10 da aure. Jarumin ya wallafa hotunansa tare da iyalansa daban-daban a shafinsa na Instagram domin raya wannan rana.
An ruwaito cewa kakakin rundunar yan sandan, Magaji Musa Majia, ya bayyana a ranar Alhamis,25 ga watan Oktoba cewa kungiyar ta sanar da hukumar shirinsu na taruwa a Gyadi-Gyadi kan Gadar Lado don fara tattakin su na 'arbaeen'.
Kakakin Jam’iyyar APC na Kasa, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa masu suka da neman a tsige shugaban jam’iyyar, Adams Oshimhole, musamman wasu gwamnoni da manyan jami’an gwamnati, suna yi ne don basu yi nasara ba.
Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya yi zargin cewa akwai wani makircin da mutanen da suka yi kane-kane a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke kullawa domin kwancewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zani a kasuwa.
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta sanar da sunayen yan takarar kujeran shugaan kasa da na majalisar dokokin kasar wanda za su kara a zaen 2019 mai zuwa. Hakan zai kawo karshen rikice-rikice wasu jam’iyyu da ya ki cinyewa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar da ke bayani kan kalubalen da ta fuskanta a wasu jihohi, Jam'iyyar All Progressives Congress ta ce tana da 'yancin mika sunayen 'yan takararta na Zamfara kuma hakkin hukumar zabe ne ta amsa.
Aisha Musa
Samu kari