Yanzu Yanzu: Buhari, Lalong, Dalung da malaman addini na ganawar sirri
- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri na kungiyar malaman Kirista
- Ganawar ya samu halartan gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong da kuma ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung
- Sauran wadanda suka halarci ganawar sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Musapha da shugaban ma’aikata, Abba Kyari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da shugabannin kungiyar Council of the Church of Christ in Nation (COCIN), Vanguard ta ruwaito.
Ganawar wanda ya samu halartan gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong da kuma ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya farad a misalin 11.31 na safe a fadar shugaban kasa Abuja a ranar Talata, 6 ga watan Nuwamba.

Asali: Depositphotos
Reverend Obed Dachung ne ya bude taro da addu’a. Cikin wadanda suka halarci ganawar harda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Musapha da shugaban ma’aikata, Abba Kyari.
A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Yarima kuma mai jiran gado a masarautar Birtaniya, Charles da uwargidarsa, Camilla sun isa babbar birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Majalisar dattawa ta kaddamar da bincike kan harin kisan da aka kaiwa Ekweremadu
Sun iso kasar ne a yau Talata, 6 ga watan Nuwamba.
Babban kwamishinan Birtaniya a Najeriya, Paul Arkwright ya sanar a Abuja a ranar Lahadi, 4 ga watan Nuwamba cewa Yarima Charles zai kasance a shirin kulla zaman lafiya, ciki harda magance matsalar hare-haren makiyaya da manoma a garuruwan Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng
Asali: Legit.ng