Har yau ba mu da dan takarar gwamna a Jihar Imo –APC
Kakakin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Lanre Issa-Onilu, ya caccaki masu shirya munakisa don ganin tsige shugaban jam’iyyar, Adams Oshimhole.
Ya bayyana wasu gwamnoni da manyan jami’an gwamnatin da suka bukaci hakan a matsayn masu son zucia cewa suna yi ne kawai don ba su yi nasara ba a zaben fidda gwani, ko kuma a ce jama’a ba su zabi san ransu ba.
Da ya ke hira da yan jarida, Lanre ya ya caccaki wasu gwamnoni, musamman na jihar Ogun, Ibikunle Amosun, wanda ya kira Oshiomhole ‘dan gada-gada.’

Asali: Depositphotos
Hakazalia ya soki shugaban gidan radiyon Najeriya da ya ambaci Osinajo a matsayin dan damfara.
Da ya ke magana a kan dan takarar gwamnan APC a jihar Imo, inda ake zargin Gwamna Rochas Okorocha ya yi karfa-karfa da banga-bangar dora sirikin sa, Uche Nwosu, Lanre ya ce har yau APC ba ta kai ga yanke hukuncin wane ne dan takarar gwamna a jihar Imo ba tukunna.
KU KARANTA KUMA: Akwai makircin da ake kullawa akan Buhari - Amosun
Ya yi nuni da cewa ranar 2 ga watan Nuwamba ne wa’adin mika wa INEC sunan dan takarar gwamna a kowace jiha zai cika, ba ranar 18 ga watan Oktoba kamar yadda INEC din ta rika jaddadawa ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Lagit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng