Sanatan Kebbi Ya Watsawa Barau Kasa a Ido da Ya So Hana Shi Sauya Sheka daga APC zuwa ADC

Sanatan Kebbi Ya Watsawa Barau Kasa a Ido da Ya So Hana Shi Sauya Sheka daga APC zuwa ADC

  • Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Garba Musa Maidoki, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa ADC
  • Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ba Maidoki baki domin ya sauya shawarar da ya yanke
  • Sanatan ya sanar da cewa rikicin cikin gida na jam'iyyar APC ya taka rawar wani wajen shawarar da ya yanke ta sauya sheka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

​FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Garba Musa Maidoki, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa ADC.

Sanata Garba Maidoki shi ne shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan bin dokokin majalisa kuma mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan yada labarai da wayar da kan al'umma.

Maidoki ya sauya sheka zuwa ADC
Sanata Garba Maidoki na jawabi a wajen taro Hoto: Sen. Garba Musa Maidoki
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Sanatan ya sanar da ficewarsa ne a cikin wata wasika da ya aikawa shugaban Majalisar Dattawa kuma aka karanta ta a yayin zaman majalisar na ranar Talata, 23 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

ADC ta tabbatar da abokin takarar Atiku bayan fara gunaguni kan zabin Amaechi

Meyasa Sanata Maidoki ya bar APC?

Sanata Maidoki ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ba a warware ba a jam'iyyar APC biyo bayan zabubbukan fitar da gwani a jihar shi ne dalilin da ya sa ya dauki wannan mataki, Vanguard ta kawo labarin.

Ya bayyana cewa shawarar tasa ta biyo bayan "shawarwari masu zurfi da ya yi da mutanen mazabarsa" kuma matsalolin da suka samo asali daga zabubbukan fitar da gwani na APC ne suka janyo ta.

“Akwai rikicin cikin gida a jam'iyyar APC, musamman wanda ya samo asali daga zabubbukan fitar da gwani na jihar Kebbi."
"Bayan shawarwari da suka dace da mutanen mazabata, na yanke shawarar sauya sheka zuwa ADC, wacce na yi amana cewa ta fi dacewa da bukatun yankina."

- Sanata Garba Maidoki

Barau ya yi kokarin shiga tsakani

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya bukaci sanatan da ya janye batun sauya shekar tasa domin ba da damar yin sasanci.

Kara karanta wannan

Siyasar Pantami ta kara karfi a Gombe da tsohon hadimin gwamna ya koma PDP

Ya bayyana cewa jam'iyyar APC a Kebbi ba ta da wani babban rikici na gaske, kuma za a iya warware korafin Maidoki a cikin gida.

“Na shiga tsakani tare da rokon sanata da ya janye shawararsa. Babu wata matsala ta cikin gida a jam'iyyar APC a jihar Kebbi. Wannan ya fi kama da sabani na cikin gida kuma za mu iya sasantawa. Ina ba da shawarar cewa a ajiye batun sauya shekar nan a gefe domin yin sulhu."

- Sanata Barau Jibrin

Sanata Maidoki ya koma ADC daga APC
Sanata Garba Musa Maidoki a zauren majalisar dattawa Hoto: Sen Garba Musa Maidoki
Source: Facebook

Maidoki ya nace kan shiga ADC

Sai dai kuma, Maidoki ya ƙi amincewa da bukatar Sanata Barau, inda ya jaddada cewa ya riga ya gama yanke shawara.

Ficewar Sanata Maidoki ta ƙara yawan jerin sauya sheka da ake samu daga APC zuwa ADC a cikin watannin baya-bayan nan.

Tsohon hadimin gwamna ya fice daga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin gwamnan jihar Gombe, Aliyu Musa, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Aliyu Musa ya koma jam'iyyar PDP ne tare da dubban magoya bayansa, a wani mataki da zai ƙara sauya yanayin siyasa a jihar Gombe.

Tsohon hadimin gwamnan ya ce shawararsa ta barin APC ta samo asali ne daga goyon bayan da yake ba Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Tags: