Majalisar Dattawa Ta Amince da Bukatar Tinubu kan Batun Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya
- Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin kafa ‘yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaron da ta addabi kasar nan
- Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Majalisar ta amince da gyaran kundin tsarin mulki don kafa yan sandan jihohi
- Rahotanni sun nun cewa kudirin ya samu goyon bayan galibin sanatoci, inda suka bayyana muhimmancin kafa rundunar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya da zai ba da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a kasar nan.
Matakin ya kasance daya daga cikin manyan sauye-sauyen da ake jira na tsarin tsaro, musamman a daidai lokacin da ake fama da kalubalen ‘yan bindiga, satar mutane da sauran matsalolin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.

Source: Facebook
Wani sanannen mai amfani da kafafen sada zumunta, Imran Mohammed ne ya wallafa labarin amincewar da Majalisar dattawa ta yi a shafinsa na X.
Amincewar majalisar na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika mata bukatar kafa rundunar yan sandan jihohi a Najeriya.
Yadda aka gabatar da kudirin a Majalisa
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ne ya gabatar da bukatar dakatar da wasu dokokin majalisa domin hanzarta duba kudirin da Tinubu ya gabatar.
Yayin da yake jagorantar muhawara kan kudirin, Bamidele ya ce manufarsa ita ce samar da rundunar ‘yan sandan jihohi tare da ci gaba da kasancewar rundunar ‘yan sandan tarayya mai ƙarfi.
Ya bayyana cewa kudirin ya tanadi kafa kwamitocin kula da aikin ‘yan sandan jihohi masu zaman kansu, ƙa’idojin aikin ‘yan sanda na kasa baki ɗaya, da kuma matakan tabbatar da gaskiya da hana amfani da iko ba daidai ba.
A cewarsa, tsarin zai taimaka wajen inganta aikin tsaron al’umma, tattara bayanan sirri da kuma saurin mayar da martani ga barazanar tsaro, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Sanatoci sun goyi bayan kudirin
Da yake bayar da gudunmawarsa, Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta sun kai matakin da ke bukatar sababbin hanyoyin magance su.
Sai dai ya bukaci a samar da matakan kariya domin hana siyasantar da rundunar ko amfani da ita wajen tauye hakkin jama’a.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi wani muhimmin mataki ne na karfafa tsarin tarayya da kuma magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
Tambuwal ya jaddada bukatar sanya dokoki masu ƙarfi domin hana duk wani amfani da tsarin ta hanyar da za ta cutar da ‘yan kasa.
Bayan samun goyon bayan mafi yawan sanatoci, Majalisar Dattawa ta amince da kudirin a karatu na biyu tare da tura shi zuwa kwamitin duka majalisa, inda aka amince da shi.

Source: Facebook
Majalisa ta rantsar da sanatoci 4
Kun ji cewa Majalisar dattawan Najeriya ta rantsar da sanatoci hudu da suka lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Sabbbin sanatocin sun maye gurfin tsofaffin wakilan mazabunsu, wadanda suka rasu da wadanda suka ajiye aiki domin karbar wani mukami.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya taya su murna tare da yi wa tsofaffin 'yan majalisar da suka rasu addu’a.
Asali: Legit.ng


