APC ta ce INEC ba ta iya dakatar da 'yan takararta a Zamfara
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta jaddada cewa ta aika da sunayen 'yan takararta ga hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC.
A cikin wata sanarwa da ta fitar da ke bayani kan kalubalen da ta fuskanta a wasu jihohi, Jam'iyyar ta ce tana da 'yancin mika sunayen 'yan takararta na Zamfara kuma hakkin hukumar zabe ne ta amsa.
Ta ce hukumar zabe ba za ta iya hana wa 'yan takararta shiga zabe ba a Zamfara.

Asali: Depositphotos
Ta kuma jadadda cewa ikirarin da hukumar ta yi kan lamarin 'yan takararta a Zamfara ba daidai ba ne don haka za ta ci gaba da bin matakan da suka dace domin tabbatar da ganin hukumar ta yi abin da ya dace.
KU KARANTA KUMA: Sanatocin APC da PDP sun kara bisa furucin da Keyamo ya yi kan Atiku
Jam'iyyar APC ta dage kan cewa tana da 'yan takara kuma tuni ta mika sunayensu ga hukumar zaben.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Lagit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng