Yajin aiki: An fara layin man fetur a Kano

Yajin aiki: An fara layin man fetur a Kano

- Sakamakon shirin shiga yajin aikin gama gari da kungiyar Kwadago ta kira an fara samun layin motoci a gidajen sayar da man da ke jihar Kano

- An gano motoci tsaye a gidajen mai domin siyan man fetur

- Gidajen mai da yawa sun kulle bisa cewar wai ana kishin-kishin din rage kudin mai don haka suka ki siyo man tukuna

Sakamakon shirin shiga yajin aikin gama gari da kungiyar Kwadago ta kira da za a fara daga ranar Talata, 6 ga watan Nuwamba, an dan fara samun layin motoci a gidajen saida mai dake jihar Kano, jaridar Premium Times ta ruwaito.

A karamar hukumar Gwarzo, an ga motoci suna tsaye a gidajen mai domin siyan man fetur. Wasu da dama daga gidajen saida man fetur din sun kulle gidajen cewa wai a dalilin kishi-kishin din da aka ji wai za a rage kudin mai shine yasa ba su sayo man ba tukuna.

Yajin aiki: An fara layin man fetur a Kano
Yajin aiki: An fara layin man fetur a Kano
Asali: UGC

Ko da yake gidajen mai a cikin garin Kano na saida mai.

Shugaban kungiyar masu hada-hadar man fetur reshen jihar Kano Bashir Dan-Malam, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai cewa wannan karanci da aka fara samu a jihar na da alaka da rade-radin rage kudin mai da ake ta yayada wa.

Ya ce wasu na ganin kamar gwamnati za ta rage kudin mai daga naira 145 zuwa naira 95 kowace lita.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 5 ga watan Nuwamba ya roki shugaban kungiyar kwadago da su duba matsalolin da gwamnatinsa ta gada.

KU KARANTA KUMA: Mutuwar Alkali: Lalong ya roki rundunar soji da ta yafe ma mutanen Plateau

Buhari ya yi rokon ne lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar jakadan Najeriya masu ritaya karkashin jagorancin Ambasada Oladapo Fafowora a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng