Rigima a Dajin Katsina, Yaran Ado Aliero na Neman Wani Dan Ta’adda Ruwa a Jallo

Rigima a Dajin Katsina, Yaran Ado Aliero na Neman Wani Dan Ta’adda Ruwa a Jallo

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa a cikin kwanaki biyu da suka gabata, an ce mabiyan Ado Aleiro na bibiyar Kachalla Muhammadu
  • Rahotanni sun nuna cewa rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu na kara tsananta, yayin da ake ci gaba da gwabza fada a yankunan
  • Wasu na ganin wannan rikici ya rage matsin lamba kan al’ummomi, domin bangarorin na raunana junansu maimakon kai hare-hare ga fararen hula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Matazu, Katsina - Wasu rahotanni sun tabbatar da ana kai ruwa rana a dazukan Matazu da Musawa da ke jihar Katsina tsakanin yan bindiga.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa alaka ta yi tsami tsakanin wani hatsabibin dan ta'adda da kuma yaran Ado Aliero.

Yaran Aliero na neman dan ta'adda ruwa a jallo
Dan ta'adda, Ado Aliero da Kachallah Muhamadu. Hoto: @DanKatsina50.
Source: Twitter

Rahoto daga shafin Bakatsina a X ya bayyana yadda yatan Aliero ke bibiyar wani dan ta'adda mai suna Kachalla Muhammadu a dazukan Matazu da Musawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sakkwato ta yi magana kan rahoton da ake yadawa game da Bello Turji

Yaran Aliero sun taso dan ta'adda a gaba

A cikin kwanaki biyu da suka gabata, majiyoyi sun bayyana cewa mabiyan Ado Aliero sun ci gaba da bibiyar Kachalla yadda bera ke farautar mage ba tare da gajiya wa ba.

Majiyoyin sun ce gaba da kiyayyar da ke tsakanin bangarorin biyu na kara tsananta yayin da kowanne bangare ke kokarin samun rinjaye.

Yayin da rikicin ke kara kamari a cikin dazukan yankin, an ce an samu saukin matsin lamba kan al’ummomin da ke kusa.

Yadda rikicin yan ta'adda ya kawo sauki ga al'umma
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda rikicin yan ta'adda ya rage hare-hare

Wasu mazauna yankunan na ganin cewa fada tsakanin kungiyoyin biyu ya rage musu damar shirya hare-hare kan jama’a.

Ana kuma ganin cewa ci gaba da arangamar tsakanin bangarorin na taimakawa wajen raunana karfinsu da rage tasirinsu.

Duk da haka, jama’a na ci gaba da fatan samun zaman lafiya mai dorewa da kuma kawo karshen matsalar rashin tsaro.

Ana ci gaba da yin addu’o’i domin Allah Ya kawo karshen tashin hankali tare da tabbatar da zaman lafiya a fadin kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi maganar da ta ba da mamaki kan tsaro

Mutane da dama na fatan hukumomi da masu ruwa da tsaki za su kara kaimi wajen samar da mafita ga matsalolin tsaro.

Haka kuma ana rokon Allah Ya kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko’ina.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar hare-haren yan ta'adda musamman a yankunan karkara a Arewa maso Yamma.

Kullum al'umma na cikin fargaba game da harin yan ta'adda yayin da ake kiran hukumomi da su dauki matakan kawo karshen lamarin da ke faruwa.

Kanin Aliero ya gwabza da sojoji a Katsina

Mun ba ku labarin cewa sojojin Najeriya sun dakile wani yunkurin harin ‘yan ta’adda a Kafur, Jihar Katsina, tare da kwato dabbobi 529 da aka sace.

Rundunar ta yi artabu da ‘yan bindigar da ake zargin sun shigo daga Zamfara, inda aka tilasta musu tserewa da barin dabbobin.

Shugabannin soji sun yaba da jarumta da kwarewar dakarun, suna tabbatar wa jama’a ci gaba da kai farmaki kan masu aikata laifi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.