Tashin hankali a Kaduna yayinda yan sanda suka kama mutum 32 kan sabon rikici
Rundunar yan sanda a jihar Kaduna sun kama mutane 32 da ake argi da hannu a sabon rikicin da ya barke a jihar.
A wata sanarwa daga kakakin gwamnan jihar, Samuel Aruwan ya bayyana cewa jami’an tsaro sun dakatar da wani yunkuri na tayar da zaune tsaye a wuraren ibada da ke unguwannin Hayin Banki da kuma Kawo a cikin garin Kadunan.
Har ila yau an kuma kashe mutum daya a Kasuwan Magani kana aka kama wani mutum da tsakar dare dauke da bindiga, in ji sanarwar.

Asali: Depositphotos
Mista Aruwan ya ce "za a gudanar da bincike kan mutanen sannan a gufrfanar da su gaban kuliya."
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaban APC a Enugu ya tsallake rijiya da baya yayinda makasa suka harbi mai tsaronsa
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta ce ta sassauta dokar hana fita a yankin Kachia inda a ranar Asabar, 27 ga watan Oktoba za a bar mutane su fita har zuwa karfe biyar na yamma.
Sannan kuma daga ranar Lahadi za su fita daga karfe shida na safe zuwa biyar na yammaci a kullum.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng