"An Ci Amanarmu": Sanata Maidoki Ya Yi Fallasa kan APC bayan Komawa ADC

"An Ci Amanarmu": Sanata Maidoki Ya Yi Fallasa kan APC bayan Komawa ADC

  • A ranar Talata, 23 ga watan Yunin 2026, Sanata Garba Musa Maidoki ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC a hukumance zuwa ADC
  • Sanatan mai wakiltar Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa ya yi zarge-zarge kan jam'iyyar APC bayan ya sauya sheka zuwa ADC mai adawa
  • Hakazalika, sanatan ya bayyana tayin da aka yi masa kafin ya shigo jam'iyyar ADC wadda ke kokarin kafa gwamnati a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Garba Musa Maidoki, ya yi zargi kan jam'iyyar APC mai mulki.

Sanata Maidoki ya zargi APC da cin amanar mambobin jam'iyya masu nagarta, biyo bayan sauya sheƙar da ya yi zuwa jam'iyyar adawa ta ADC.

Sanata Maidoki ya ce APC ta ci amanarsa
Sanata Garba Maidoki na jawabi a zauren Majalisar Dattawa Hoto: Sen Garba Musa Maidoki
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce Maidoki ya yi waɗannan kalamai ne ranar Talata, 23 ga watan Yunin 2026 yayin da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan ya sanar da ficewarsa a hukumance daga jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Sanatan Kebbi ya watsawa Barau kasa a ido da ya so hana shi sauya sheka saga APC zuwa ADC

Meyasa Sanata Garba Maidoki ya koma ADC?

Sanata Maidoki ya ce shawarar komawarsa ADC samo asali ne daga abin da ya bayyana da gurɓacewar dimokuradiyyar cikin gida a jam'iyyar APC da kuma ƙaruwar tasirin uban-gida a siyasa.

“Abin da suke kira zaɓen fitar da gwani na maslaha bai tsaya ga APC kaɗai ba. Kusan a dukkan jam'iyyun siyasa, wani tsari ne inda shafaffu da mai ke sanya yaransu a muƙamai ba tare da la'akari da sauran 'yan Najeriya ba."

- Sanata Garba Musa Maidoki

A cewar Sanatan, tsarin zaɓen 'yan takara na APC a jihar Kebbi ya kasance ƙarƙashin ikon wasu masu fada-a-ji waɗanda suka zabi 'yan takarar da suke so tare da hana dama ga sauran masu neman takara, Platinum Tv ya sanya hirar a Facebook.

Me Maidoki ya ce kan APC?

Yayin da yake nuna bacin rai kan wannan lamari, Maidoki ya ce mambobin jam'iyya da dama sun ji an yi watsi da su duk da sadaukarwar da suka yi wajen ƙarfafa dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

ADC ta tabbatar da abokin takarar Atiku bayan fara gunaguni kan zabin Amaechi

“Mun ji an ci amanarmu. Mun ji an ci amanarmu cewa, duk da mafi kyawun ƙoƙarinmu na ganin dimokuradiyya ta yi aiki a ƙasar nan, abin takaici, dimokuradiyya a Najeriya tana cikin wani mawuyacin hali."

- Sanata Garba Musa Maidoki

Sanata Maidoki ya koma jam'iyyar ADC
Sanata Garba Maidoki a zauren Majalisar Dattawa Hoto: Sen Garba Musa Maidoki
Source: Facebook

An yi wa Maidoki tayin tikiti a ADC

Sanatan ya bayyana cewa komawarsa ADC ta zo cikin sauki ne sakamakon ɗan takarar jam'iyyar, ya janye bisa radin kansa domin ba shi damar yin takara a inuwarta.

“Mutumin da ya lashe zaɓen fitar da gwani na ADC ya kira ni ya ce, 'Oga, na sani ba za su ba ka tikiti ba. Ka dawo, zan ba ka nawa tikitin takarar.' Wannan karamcin nasa ya taba ni sosai."

- Sanata Garba Musa Maidoki

APC ta aika sako ga Gwamna Oyebanji

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta aika sako ga gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji kan nasarar da ya samu a zabe.

Jam'iyyar APC ta taya Biodun Oyebanji murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar Ekiti na ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

APC ta bayyana cewa nasarar Biodun Oyebanji cike take da tarihi, domin ya zama gwamnan farko da ya yi tazarce a jihar Ekiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng