Kannywood: Lawan Ahmed ya yi bikin cika shekara 10 da aure
A ranar Alhamis, 25 ga watan Oktoba, jarumin Kannywood, Lawan Ahmed ya yi bikin cikarsa shekara 10 da aure.
Jarumin ya wallafa hotunansa tare da iyalansa daban-daban a shafinsa na Instagram domin raya wannan rana.
A daya daa cikin hotunan ya rubuta “Alhamdulillah a yau ya yi daidai da cikarmu shekara 10 da aure, Allah ya ci gaba da sanya albarka a wannan iyalai. Ameen.”

Asali: UGC
Lawan wanda ya kasance daya daga cikin shahararrun fuskki a Kannywood, ya fito a manyan fina-finai tare da Ali Nuhu.
KU KARANTA KUMA: Akwai barazanar yunwa a Jigawa sakamakon hare-haren da kwari ke kaiwa gonakin shinkafa
Ya kuma fito a fina-finai da dama kamar su: “Mikiya”, “Dama Tace”, “Zan Rayu Dake” da sauransu.
A hotunan a nuno shi, matarsa da kuma yaransa guda uku, maza biyu mace guda.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng