Atiku zai je kasar Amurka a karshen Nuwamba - Okupe
- Doyin Okupe ya bayyana cewa dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai je kasar Amurka a karshen Nuwamba
- Ya bayyana haka a shafinsa na twitter a ranar Lahadi, 4 ga watan Nuwamba
-A halin yanzu Atku ya bayyaa cewa ya shirya zuwa Amurka a yanzu, idan har hukumomin diflomasiyya suka amince da bizar sa
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Doyin Okupe ya bayyana cewa dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Alhaji Atiku Abubakar zai je kasar Amurka a karshen Nuwamba.
Okupe wanda ya kuma kasance tsohon kakakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana haka a shafinsa na twitter a ranar Lahadi, 4 ga watan Nuwamba.

Asali: Depositphotos
Ku tuna cewa wasu masu sukar Atiku sun yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ba zai iya zuwa kasar Amurka ba saboda zargin sa da laifi da kasar ke yi.
KU KARANTA KUMA: EFCC da yan sanda sun kai mamaya coci sun kama fasto kan damfara
Legit.ng ta ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najriya Atiku Abubakar wanda ya gaza zuwa Amurka tun bayan barinsa mulki a 1999, ya bayyaa cewa ya shirya zuwa Amurka a yanzu, idan har hukumomin diflomasiyya suka amince da bizar sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng