Wike Ya Aika Sako ga Super Eagles kan Gaza zuwa Gasar Cin Kofin Duniya

Wike Ya Aika Sako ga Super Eagles kan Gaza zuwa Gasar Cin Kofin Duniya

  • Ana ci gaba da buga wasanni a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 a kasashen Amurka, Canada da Mexico
  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya nuna rashin jin dadinsa saboda rashin kasancewar Najeriya a gasar
  • Wike ya bayyana cewa kasashen da ba a sansu ba ma sun samu gurbi a gasar amma Najeriya kuwa ta gaza zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana bacin ran 'yan Najeriya game da gazawar da tawagar Super Eagles ta yi na samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA na shekarar 2026.

Wike ya bukaci tsohon kyaftin din kungiyar, Joseph Yobo, da ya isar da wannan bacin ran na jama'a ga 'yan wasan Super Eagles.

Wike ya ce bai ji dadin rashin ganin Najeriya a gasar cin kofin duniya ba
Nyesom Ezenwo Wike, Ministan babban birnin tarayya Abuja Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa Wike ya yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da titin Kuje zuwa Gwagwalada a Abuja a ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Israila ta shirya bijirewa Amurka kan Lebanon

Tsohon kyaftin din na Super Eagles, Joseph Yobo yana daya daga cikin manyan baki da suka halarci taron.

Wike ya koka kan rashin Najeriya a World Cup

Ministan ya ce 'yan Najeriya da dama har yanzu ba su farin ciki da cewa kasar ba za ta shiga gasar cin kofin duniya ba duk da cewa an fadada gasar zuwa kasashe 48 sannan kuma ga shi akwai 'yan wasan Najeriya a manyan gasar wasanni a fadin duniya.

“Amma kafin na bar wannan waje, muna taya daya daga cikin taurarinmu murna, wato Joseph Yobo. Amma bari na yi amfani da wannan dama ta hanyarka domin na shaida wa Super Eagles cewa ba mu farin ciki."
“Don haka idan babu wanda ya fada muku hakan, saboda akwai wasu mutane da ke tafa muku."

- Nyesom Wike

Ya ce kasashen da ba a sani ba sun je

Ministan ya nuna takaicinsa kan yadda kasashen da ba su kai Najeriya tarihi a harkar kwallon kafa ba suka samu gurbi a gasar cin kofin duniya yayin da Najeriya ta gaza kaiwa, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Malamar Islamiyya: Sufeton 'yan sanda ya dauki mataki kan DPO a Kaduna

“Ina kallon gasar cin kofin duniya kuma kasashen da ban taba jin sunansu ba a baya sun samu gurbin buga gasar cin kofin duniya."
“Kuma ina zama na tsawon sa'o'i ina kallon kasashen da ba a san su ba. Najeriya, a wannan gabar, tana da akalla 'yan Najeriya 13 da ke buga wasa a fadin duniya (a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa yanzu). Amma a nan, mu ba mu cancanci shiga ba."

- Nyesom Wike

Wike ya koka kan rashin zuwan Najeriya gasar cin kofin duniya
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Wane sako ya aika wa Super Eagles?

Yayin da yake magana kai-tsaye ga Yobo, Wike ya ce:

“Yobo, ka je ka shaida masu cewa ba mu farin ciki, ba mu ji dadi ba."

Najeriya ta rasa gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta shekarar 2026 ne bayan ta gaza yin abin kirki a wasannin neman gurbin shiga gasar na nahiyar Afirka, duk da cewa an fadada gasar daga kasashe 32 zuwa 48.

Wike ya magantu kan tazarcen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike, ya nuna goyon bayansa ga nasarar Bola Tinubu a babban zaben shekarar 2027 da ke tafe a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki manoma a Kaduna, an kashe bayin Allah

Ministan na babban birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa Rivers ba ta da wani zaɓi face ta ci gaba da mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake samun nasara a zaɓen 2027.

A cewarsa, daga shekarar 2023 zuwa yanzu, Rivers ta samu muƙamai da damammaki masu yawa, saboda haka ya kamata jama'a su nuna godiya ga shugaban ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng