Kotu ta ba Orji Kalu kwanaki 7 ya gurfana a gaban ta

Kotu ta ba Orji Kalu kwanaki 7 ya gurfana a gaban ta

Babbar kotun tarayya da ke Lagas ta ba wani tsohon Gwamna kwanaki bakwai dmin ya gurfana a gaban ta. Alkalin babbar kotun, Justis Mohammed Idris ya bayar da umurnin ne a ranar Litinin bayan an dawo zama domin ci gaba da sauraron karar a Lagas.

Kalu wanda bai halarci zaman ba na fuskantar shari’a kan zargin zambar naira biliyan 7.65.

Lauyan sa, Farfesa Awa Kalu (SAN) ya fada ma justis Idris cewa wanda yake karewa na a kasar Jamus inda ake masa aiki.

Ya kara da cewa likitocin tsohon gwamnan ne suka bayar da shawarar cewa ya ci gaba da kasancewa a Jamus na dan wani lokaci domin ya samu lafiya sosai.

Kotu ta ba Orji Kalu kwanaki 7 ya gurfana a gaban ta
Kotu ta ba Orji Kalu kwanaki 7 ya gurfana a gaban ta
Asali: Depositphotos

Lauyan dake kare wanda ake kara ya fada ma kotu cewar lauyan me kara, Mista Rotimi Jacob (SAN, na sane da lamarin sannan ya bukaci Justis Idris da ya sake dage shari’an.

Amma lauyan EFCC, Jacobs yace yayi mamakin rashin kasancewar Kalu a kotu, inda ya kara da cewa bai san ko tsohon gwamnan ya samu yardan kotu na yin tafiya ba.

Jacobs ya bayyana cewa tunda fasfot dinsa na daga cikin ka’idan beli, ya zama dole Kalu ya nemi kotu ta basa fafot dinsa a duk lokacin da zai tafi waje.

Da yake bayyana rashin hallaran tsohon gwamnan a matsayin son jan shari’an, Jacob ya bukaci Justis Idris da ta dubi rashin hallaran Kalu a matsayin tsere ma beli.

KU KARANTA KUMA: Dariye ya nuna goyon baya ga Buhari da Lalong daga gidan yari

Don haka alkali Odris ya ba Kalu kwanaki bakwai ya dawo daga Jamus sannan ya gurfana a gaban sa.

An dage shari’an zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba domin ci gaba da shari’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng