Kwamitin Shugaban Kasa ba shi da karfin ikon kwace kadarori da gurfanarwa – Kotun daukaka kara
Wata kotun daukaka kara a birnin tarayya, Abuja ta karbe karfin ikon kwamitin Shugaban Kasa mai Kwato Kadarori da gurfanar da wadanda ake zargi kotu.
Alkalai biyar karkashin jagorancin Alkali Hussein Mukhtar ne suka zartar da hukuncin cewa kwamitin shugaban kasar bai da ikon nufar kotu kan lamarin wani da ake zargi da mallakar manyan kadarori da kuma gurfanar da shi.
Wannan hukunci ya zuwa ne biyo bayan wata kara da wani ma’aikacin gwamnati mai suna Tijjani Tumsah ya shigar.
Tumsah, wanda ma’aikaci ne a Ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje, ya shigar da karar ce ta hannun lauyan sa mai suna Kehinde Ogunwumiju(SAN).

Asali: Depositphotos
Ya shigar da karar ne bayan kwamitin ya kwace masa wasu kadarori kuma an shigar da shi kara kotu.
Ya ce kotu ta ce aikin kwamitin ba ya na nufin har da saurin kwace kadarorin jama’a kai tsaye ba tare da shari’a ta tabbatar da su a matsayin masu laifi ba.
KU KARANTA KUMA: Mambobin JTF 103 sun shiga aikin soja, an basu kudade da filaye
Don haka kwamitin ba shi da hurumin kwace kadarori, kuma ba shi da ikon gurfanar da wadanda ake zargi a kotu.
Kotun ta ce bincike ne kawai aikin kwamitin, kuma a iyar bincike ya kamata ya tsaya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng
Asali: Legit.ng