Ku shirya karban sakamako – Rundunar soji ta yi sabon gargadi ga yan Shi’a

Ku shirya karban sakamako – Rundunar soji ta yi sabon gargadi ga yan Shi’a

- Rundunar soji ta gargadi ýan Shi'a akan rikicin da suke yi da su a fadin kasar

- Mambbin kungiyar Shi’a sun kara da sojoji a wasu yankuna na babbar birnin tarayya Abuja a makon da ya gabata

- A cewar rundunar duk wata kungiya dake shirin yin fito-na-fito da sojojin kasar toh sui shirya karban sakamako

John Agim, kakakin hedkwatar hukumar tsaro, ya fada ma mambobin kungiyar musulmai na ýan shi’a da su shirya sakamakon duk abun da suka yi ma sojoji.

Mambbin kungiyar Shi’a sun kara da sojoji a wasu yankuna na babbar birnin tarayya Abuja a makon da ya gabata.

Rundunar soji ta tabbatar da cewar an kashe yan Shi’a uku, yayinda sojoji hudu suka ji rauni. amma kungiyar sun kaddamar da cewa basu ga mambobinsu 1,000 ba.

Ku shirya karban sakamako – Rundunar soji ta yi sabon gargadi fa yan Shi’a
Ku shirya karban sakamako – Rundunar soji ta yi sabon gargadi fa yan Shi’a
Asali: Twitter

Da yake hira da Osasu Igbinedion cikin shirin The Osasu Show, Agim ya karyata zargin cewa an tura sojoji domin su hargitsa zanga-zzangarsu, cewa wadanda suke zargin sojin na son shafa masu bakin fenti ne.

Da aka tambaye shi kan dalilin da yasa ake so yan shi’a su bi doka alhalin gwamnatin tarayya ta ki bin umurnin kotu wajen sakin Zakzaky, Agim ya ce: “Wato suna kai wa sojoji hari don nuna rashin amincewarsu da gwamnati ne? Toh su shirya karban sakamako.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa sanatocin APC suka ki tsige Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa – Shehu Sani

“Ba mu da alburushin roba a duk lokacin da aka tura mu aiwatar da aiki. Don haka duk wata kungiya da bata farin ciki da gwamnati kuma suke son gwadawa akan dojoji, toh su shirya fuskantar sakamako.

“Duk wata matsala da yan shi’a ke da shi tsakaninta da gwamnatin tarayya, toh su yi shi bisa tsarin mulki da doka. Idan har ka tunkari kowani soji a duniya toh zaka durkushe ne.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng