2019: INEC ta haramtawa jami’anta shiga kungiyoyin WhatsApp

2019: INEC ta haramtawa jami’anta shiga kungiyoyin WhatsApp

- An haramta wa jami’an hukumar zabe mai zaman kanta shiga kungiyoyin shafin sadarwa na WhatsAPP

- Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da hukumar zaben ta aikewa kwamishinoninta na jiha 37 a fadin kasar ciki harda babban birnin tarayya

- INEC ta ce kada jami’anta su kuskura su bude irin wannan kungiya a shafin zumunta duk rintsi

Yayinda zaben 2019 ke gabatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta haramta wa jami’an kasancewa mamba a kungiyoyin WhatsApp.

Punch ta ruwaito cewa hukumar zaben ta aika da wata wasika ga dukkanin kwamishinonin zabe 37, inda take sanar masu hukuncin da ta yanke.

2019: INEC ta haramtawa jami’anta shiga kungiyoyin WhatsApp
2019: INEC ta haramtawa jami’anta shiga kungiyoyin WhatsApp
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa INEC ta kuma ce ta bukaci jami’anta da kada su kuskura su bude wata kungiya a shafukan zumunta.

A cewar rahoton, akwai kungiyoyi daban-daban da jami’an suka bude, inda ake tattauna lamuran da suka shafi jin dadinsu, ka’idojin aikinsu da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Shi’a: Jakadan Ingila ya koka da yadda ake kashe mutane a Najeriya

Wasu jami’ai da suka nemi a boye sunansu sunce wasu ma’aikata ne suka bude kungiya ta WhatsApp domin tattauna wasu abubuwa da suka shafi rabon kudi. Wasu kuma sun yi ikirarin cewa shugabanninsu sunyi masu sauyi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng