Fashi da Makami: An Yanke wa Wasu 'Yan Najeriya 3 Hukuncin Kisa, Za a Rataye Su

Fashi da Makami: An Yanke wa Wasu 'Yan Najeriya 3 Hukuncin Kisa, Za a Rataye Su

  • Kotu ta yankewa mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin fashi da makami a wani kamfanin iskar gas
  • Wadanda aka yankewa hukuncin sun hada da Uche Onu, Ekene Okorie da Celestine Eze, wadanda aka same su da laifin fashi da makami
  • Kotun ta bayyana cewa masu gabatar da kara sun kawo kwararan hujjoji da suka tabbatar da laifin, don haka ya bada umarni a rataye su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ondo - Babbar Kotun Jihar Ondo da ke Akure ta yankewa mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan same su da laifin fashi da makami.

Wadanda aka yankewa hukuncin sun hada da Uche Onu, Ekene Okorie da Celestine Eze, wadanda kotun ta same su da laifin aikata fashi da makami a wani kamfanin iskar gas da ke Akure.

Kara karanta wannan

Malamar Islamiyya: Sufeton 'yan sanda ya dauki mataki kan DPO a Kaduna

Kotu ta yanke wa wasu mutane 3 hukuncin kisa ta hanyar rataya
Wasu matasa da aka gurfanar a gaban kotu. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Yadda mutanen suka yi fashi a 2024

Kotun ta yanke hukuncin ne bisa tanadin dokar 'Fashi da makami da amfani da makamai', wadda ta haramta fashi da makami da kuma amfani da makamai wajen aikata laifi, in ji rahoton Daily Trust.

An tuhumi mutanen ukun ne da aikata fashin a kamfanin Gasland Nigeria Limited, Akure, da misalin karfe 3:00 na daren ranar 25 ga Afrilu, 2024.

An zarge su da shiga kamfanin tare da kwace babbar tukunyar gas da mota. Rahotanni sun ce a yayin harin sun kama jami’in tsaron da ke aiki a wurin, suka buga masa wani karfe a kansa.

'Yan sanda sun gudanar da bincike

Daga baya ‘yan sanda sun kama wadanda ake tuhumar na farko da na biyu a Benin, inda aka same su da motar da aka sace, amma ba su iya bayar da gamsasshen bayani kan mallakarta ba.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Gwamnatin Tinubu ta kawo shaidu 30 da za su ba da shaida a kotu

Bayan kama su, ikirarin da suka yi a lokacin bincike ya taimaka wajen gano wanda ake zargin ya tsara aikin, watau Celestine Eze.

Haka kuma, Ekene Okorie ya jagoranci jami’an bincike zuwa Jihar Legas inda aka gano babbar tukunyar gas din da aka sata.

Sai dai rahoton jaridar Punch ya nuna cewa 'yan sanda ba su yi nasara a kokarin kama sauran mutanen da ake zargin suna cikin kungiyar ba.

Yadda shari'ar wadanda ake zargi ta kasance

Kotu ta samu matasa 3 da laifin fashi da makami a Ondo, ta yanke masu hukuncin kisa.
Taswirar jihar Ondo inda aka yanke wa mutane 3 hukuncin kisa. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dukkan wadanda ake tuhumar sun musanta cewa suna da hannu a fashin da aka yi. Uche Onu ya shaida wa kotu cewa an kama shi ne a Onitsha yayin da yake tattara karafa a matsayin dan jari bola.

Shi kuma Ekene Okorie ya ce an kama shi ne kusa da wani wurin gyaran mota a Jihar Anambra. Celestine Eze ya bayyana cewa an kama shi a Onitsha inda yake aikin gyaran lantarki.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a William Olamide ya ce hujjojin da aka gabatar a gaban kotu sun tabbatar da cewa an aikata fashi da makami, kuma wadanda ake tuhumar suna dauke da makamai a lokacin gudanar da aikin.

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

Saboda haka, kotun ta yanke musu hukuncin shekaru bakwai a gidan yari kan laifin hada baki, sannan ta yankewa kowanne daga cikinsu hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin fashi da makami.

An yanke wa Hauwa hukuncin kisa

A wani labari, mun ruwaito cewa, babbar kotun tarayya da ke jihar Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin ta’addanci.

Kotun ta samu matar da laifin safarar harsasai 438 zuwa wani shugaban ‘yan bindiga da ke maboyarsa a dajin Dunburum.

Hukumar DSS ta kama Hauwa’u Mukhtar a tashar mota ta Jibia a shekarar 2023 yayin da ake zargin tana kai harsasai Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com