INEC za ta sanar da yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokoki a yau

INEC za ta sanar da yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokoki a yau

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta sanar da sunayen yan takarar kujeran shugaan kasa da na majalisar dokokin kasar wanda za su kara a zaen 2019 mai zuwa.

Hakan zai kawo karshen rikice-rikice wasu jam’iyyu da ya ki ci ya ki cinyewa tun bayan kammala zaben fidda gwani.

Duk da zabukan fidda gwani da suka gabatar, jam’iyyun siyasa da dama ciki harda APC da PDP sun ci bayyana sunayen yan takaransu kai tsaye a wasu mazabu saboda kwantar da tarzoma.

INEC za ta sanar da yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokoki a yau
INEC za ta sanar da yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokoki a yau
Asali: Depositphotos

Anyi zargin cewa duk da cewar wasu yan takara sun san cewa a su yi nasara a a zaben fidda gwani, anyi zargin cewa na sauya sunayensu da alkalami a hanyar zuwa hedkwatar INEC, Auja, wato kenan ana iya jin sunayensu a yau.

KU KARANTA KUMA: Hadimin wani gwamnan PDP ya yi murabus ya kuma fice daga jam’iyyar

A cikin jadawalin da hukumar zaben ta fitar na zaben 2019 a farkon shekarar nan ya nuna cewa za ta wallafa sunayen yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokoki a yau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Lagit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng