An Fara Sabuwar Fafutukar Neman Karin Albashi Mai Tsoka a Najeriya

An Fara Sabuwar Fafutukar Neman Karin Albashi Mai Tsoka a Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun buƙaci a ƙara masu albashi da kashi 400 cikin 100 a kan N70,000 na yanzu
  • Ma'aikatan sun bayyana cewa tsadar rayuwa ta jefa da yawa daga cikin su a mawuyacin hali, ta inda N70,000 ba za ta tsinana masu komai ba
  • A cikin jerin bukatun da ta gabatar, kungiyar ma'aikata ta nemi gwamnati ta farfaɗo da tattalin arziki, ƙarfafa darajar Naira da inganta makamashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun - Ma’aikatan gwamnati ƙarƙashin ƙungiyar haɗin gwiwa ta JNPSNC sun buƙaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su amince da ƙarin albashi da kashi 400 cikin 100.

Sun neni a masu kari kan mafi ƙarancin albashin ƙasa na N70,000 da ake biya a yanzu, domin rage raɗaɗin matsin tattalin arzikin da ‘yan ƙasa ke fuskanta.

Kara karanta wannan

An bukaci jihohi 26 su shirya saboda fargabar ambaliyar ruwa a 2026

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na jawabi ga 'yan Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa an cimma wannan matsaya ne a ƙarshen wani taron kwana biyu na ƙasa da na ƙungiyar da aka gudanar a cibiyar taruka ta Oasis da ke Osogbo a jihar Osun.

Karin albashi da a ke so

A cikin sanarwar da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Benjamin Uyanto ya sanya wa hannu, sun nuna damuwa kan yadda ma'aikata ke kara shiga damuwa, inda suka ce ma’aikata da dama na fama da tsadar rayuwa.

Sanarwar ta ce halin tattalin arzikin ƙasar ya jefa ma’aikata da iyalansu cikin mawuyacin hali, wanda ke buƙatar gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa.

“Gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su ɗauki matakan tallafi domin rage wannan wahala da ma’aikata ke ciki.

"Saboda haka, muna kira ga gwamnatoci a dukkan matakai su gaggauta amincewa da aiwatar da ƙarin albashi da ya kai kashi 400 cikin 100 kan mafi ƙarancin albashi na naira 70,000 domin magance matsalolin tattalin arzikin da ke addabar ma’aikata da iyalansu,”

Kara karanta wannan

Saudiyya ta fara rabon tallafin abinci a Najeriya, an ji wadanda za su amfana

In ji sanarwar

Ana son fara batun karin albashi

Yayin taron, an buƙaci gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago su fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi daga watan Yuli na shekarar 2026, gabanin lokacin sake duba albashi da doka ta tanada a farkon shekarar 2027.

Ƙungiyar ta bayyana cewa fara tattaunawa da wuri zai taimaka wajen kauce wa jinkiri, rashin yarda da kuma rikice-rikicen da kan biyo bayan bitar albashi.

Zanga zangar karin albashi
Lokacin da aka yi zanga-zangar neman karin albashi a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadi ga jihohi kan albashi

Dangane da aiwatar da mafi ƙarancin albashin naira 70,000, ƙungiyar ta nuna rashin jin daɗi kan yadda wasu gwamnatocin jihohi ba su aiwatar da hakan ba.

The Guardian ta wallafa cewa kungiyar ta yi gargaɗin cewa shugabancin ƙungiyar na ƙasa zai ɗauki “tsauraran matakai” kan duk wata gwamnatin jiha da ta ƙi aiwatar da karin albashi.

An rage albashi a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnain jihar Taraba karkashin Agbu Kefas ta rage albashin ma'aikata masu sharar titi da kaso mai tsoka.

Kara karanta wannan

An shigar da korafi wajen INEC domin neman hana Tinubu takarar 2027

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta zaftare albashin ma'aikatan daga N15,000 zuwa N10,000 saboda wasu matsaloli.

Ma'aikatar tsaftace muhalli ta jihar Taraba ta ce duk wanda sabon tsarin bai masa ba zai iya barin aikin ya koma neman abinci ta wata hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng