‘An Yi Masa Karya’: Hadimin Tinubu Ya Kare Shi kan Alkawarin Gyara Wuta

‘An Yi Masa Karya’: Hadimin Tinubu Ya Kare Shi kan Alkawarin Gyara Wuta

  • Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya kare mai gidansa game da karairayi da ake yadawa
  • Onanuga ya ce an karkatar da kalaman Tinubu da ya yi a shekarar 2022, yana mai cewa maganar ta kasance da sharadi ne
  • Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta dauki matakai masu muhimmanci wajen gyaran bangaren wutar lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kai, Bayo Onanuga, ya yi watsi da wasu ikirari da ake yadawa.

Ana zargin cewa Shugaba Tinubu ya yi alkawarin ba zai sake neman wa’adi na biyu ba idan har bai samar da ingantacciyar wutar lantarki ba.

Hadimin Tinubu ya musanta karairayi da ake yi wa shugaban kasa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

A wata hira da ya yi da tashar Arise News, Onanuga ya ce an yi kuskuren fassara kalaman shugaban.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta tanka da Peter Obi ya nemi Tinubu ya yi murabus

Tuna baya kan maganar Tinubu game da wuta

Ya tuna cewa a wani taron ‘yan kasuwa da aka gudanar a shekarar 2022, Tinubu ya yi magana kan matsalar lantarki.

Sai dai Onanuga ya ce masu sukar shugaban kan dauki wani bangare na jawabinsa kawai ba tare da duba cikakken mahallin maganar ba.

Ya ce shugaban bai taba cewa kai tsaye ba cewa ba zai sake tsayawa takara idan wutar lantarki ba ta inganta ba.

A cewarsa, Tinubu ya bayyana cewa idan ya gaza cimma burinsa saboda matsalolin da ya gada, ya kamata a fahimce shi.

Matakan da Tinubu ya dauka kan matsalar wutar lantarki
Shugaba Bola Tinubu da sabon ministan makamashi, Joseph Tegbe. Hoto: @StateHouse/x.
Source: UGC

Wutar lantarki: Matakan da Tinubu ya dauka

Onanuga ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta dauki matakai masu muhimmanci domin gyara bangaren wutar lantarki tun bayan hawanta mulki.

Ya bayyana sanya hannu kan Dokar Wutar Lantarki a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin gwamnatin shugaban.

Dokar ta bai wa jihohi damar samarwa, rarrabawa da kuma jigilar wutar lantarki cikin sauki a karkashin sababbin tsare-tsare.

Kara karanta wannan

Trump ya kawo tsarin da kayan abincin Amurka zai rika zuwa Iran

Ya ce hakan ya bude kofar gasa da zuba jari, kuma wasu jihohi sun riga sun fara cin gajiyar damar.

Duk da haka, ya amince cewa har yanzu kasar ba ta kai matakin samar da wutar da shugaban ya yi fata ba.

Ya danganta matsalar da karancin iskar gas, bashin da ya haura tiriliyan hudu da kuma tsohuwar cibiyar jigilar lantarki.

Onanuga ya ce gwamnatin Tinubu na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare domin kara yawan wutar lantarki da inganta rarraba ta.

Ya jaddada cewa duk da kalubalen da ake fuskanta, gwamnati na nan daram wajen cika alkawarinta na inganta bangaren lantarki.

Hadimin Tinubu ya magantu kan matsalar tsaro

Mun ba ku labarin cewa Fadar shugaban kasa ta ce Najeriya ba ta karkashin hannun 'yan ta'adda kamar yadda 'yan jam'iyyun adawa ke fada a kwanan nan.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce hare-hare da garkuwa da mutane suna faruwa ne a wasu wurare a kasar.

Onanuga ya kara da cewa duk da korafin da ake yi, ‘yan Najeriya da dama na ci gaba da tafiye-tafiye zuwa jihohin kasar cikin aminci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.