Lamari Ya Girma, Sarkin Musulmi Ya Ayyana Addu'o'i saboda 'Makiyan Najeriya'
- Kungiyar JNI karkashin jagorancin Sarkin Musulmi ta bukaci Musulmi su yi addu’ar neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya
- Sultan Sa’ad Abubakar III ya ce yanayin rashin tsaro a kasar na kara tabarbarewa, inda ya bukaci hadin gwiwa tsakanin jama’a da jami’an tsaro
- JNI ta yi kira ga yin addu’a a lokacin Tasu’a da Ashura domin neman kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga, masu tayar da kayar baya da masu garkuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Sokoto - Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta yi kira ga Musulmi su gudanar da addu’o’i domin neman taimakon Allah kan kalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Kungiyar ta bayyana cewa za a yi addu’o’in ne domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen matsalolin tsaro da sauran kalubalen da ke addabar kasar.

Source: Twitter
Sarkin Musulmi ya tunar da al'umma
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
A cikin sanarwar, JNI ta ce sarkin ya bukaci Musulmi su kasance masu tsoron Allah, masu biyayya ga dokoki, masu zaman lafiya da kuma jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
Sultan Sa’ad Abubakar ya ce ya kamata Musulmi su kasance masu kyakkyawan fata tare da dogaro da Allah wajen shawo kan matsalolin da kasar ke ciki.
A cewar sa, irin yadda Allah ya kubutar da Annabi Musa (A.S) da jama’arsa daga zaluncin Fir’auna, haka ya kamata a nemi taimakonSa wajen kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga, masu tayar da kayar baya da masu garkuwa da mutane.
An nemi a yi addu’a kan matsalar tsaro
JNI ta bayyana cewa ya zama wajibi a yi amfani da lokacin Tasu’a da Ashura wajen yin addu’o’i na musamman domin neman Allah ya kawo karshen dukkan wadanda ke kawo wa Najeriya barazana.
Kungiyar ta kuma bukaci jama’a su ci gaba da neman gafarar Allah ta hanyar tuba da yin Istighfari, tana mai cewa hakan na daga cikin hanyoyin samun sauki daga matsaloli.
Wannan kira na JNI ya zo ne yayin da Sarkin Musulmi ya bayyana damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro da yanayin tafiyar da al’amura a Najeriya ke kara yin muni, in ji rahoton Punch.
Sultan ya ce sabon salon hare-haren rashin tsaro na ci gaba da kalubalantar hanyoyin da ake amfani da su wajen magance matsalar.

Source: Getty Images
Kira ga hadin kai wajen magance matsalar
Mai alfarman ya bukaci ‘yan Najeriya su hada kai da jami’an tsaro domin taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a kasar.
Sarkin Musulmi ya jaddada cewa yaki da rashin tsaro ba aikin gwamnati da jami’an tsaro kadai ba ne, inda ya bukaci jama’a su bada gudummawa wajen samar da bayanan da za su taimaka wajen kare kasa.
Abin da ke rura wutar rikici
A wani labari, mun ruwaito cewa, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya yi karin haske kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.

Kara karanta wannan
Janar Abdulsalam ya sanya yada labaran karya cikin abu 2 da ke rura witar rashin tsaro
Sarkin Musulmin ya nuna illar da ke tattare da yin watsi da matasa wadanda ke rayuwa a cikin al'umma ba tare da samar musu da abin dogaro da kai ba.
Hakazalika babban basaraken ya bayyana cewa karfafa matasa ta hanya koya musu sana'o'i ba karamin amfani zai yi wa al'umma ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

