Dalilin da ya sa muka dakatar da tattakin yan shi’a a Kano – Yan sanda
Rundunar yan sandan jihar Kano ta nemi mabiya kungiyar Shi’a da su sauya tattakin da suka shirya yi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin rundunar yan sandan, Magaji Musa Majia, ya bayyana a ranar Alhamis,25 ga watan Oktoba cewa kungiyar ta sanar da hukumar shirinsu na taruwa a Gyadi-Gyadi kan Gadar Lado don fara tattakin su na 'arbaeen'.
Legit.ng ta tattaro cewa Majia ya ce an kin amincewa da bukatar nasu saboda wajen da suka nemi yin taron ba masallaci bane sai ya kasance babban mashigin Kano daga hanyoyin Zaria da Maiduguri.

Asali: Depositphotos
A cewarsa duk wani taro a wannan waje zai haifar da cunkoso da rashin walwala a tsakanin jama’a.
KU KARANTA KUMA: Fayose ya gaza cika ka’idojin belin da kotu ta gindaya
Ya ce indai a masallaci ne inda babu wanda zai takura an basu izinin udanar da hakan amma indai a Gadar Lado ne toh babu halin yin hakan.
A wani lamari na daban mun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta sake mayar da dokar hana fita na sa’o’i 24 a birnin Kaduna da kewayenta, Kasuwan Magani, Kajuru, Kateri da kuma Kachia.
Wannan doka zai fara aiki ne daga karfe 11 na safiyar yau Juma’a, 26 ga watan Okotoba har illa-ma-shaa’a.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng