Kofar Arziki: An Gano Ma'danai Akalla 6 Masu Daraja a Wani Yankin Jihar Kaduna
- Gwamnatin Tarayya ta sanar da gano wani yankin mai tarin ma’adanai masu daraja a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya
- Ta bayyana cewa an gano ma’adanai kamar karfen platinum, zinari, azurfa, jan karfe, lithium da wani ma'adani da ake kira 'rare earth elements'
- Alake ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da gyare-gyare domin bunkasa bangaren ma’adanai a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya sanar da wani babban ci gaba da aka samu a bangaren ma’adanai bayan gano wani yanki mai cike da tarin ma'adanai masu daraja a jihar Kaduna.
Alake ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin bude taron African Natural Resources and Energy Investment Summit 2026 da aka gudanar a Abuja mai taken “One Africa, One Resource Vision.”

Source: Facebook
An gano ma’adanai masu daraja
Punch ta ruwaito cewa ministan ya ce Hukumar Binciken Kasa ta Najeriya (NGSA) ta tabbatar ya gano tarin ma’adanai masu muhimmanci da daraja a duniya.
Daga cikin rukunin ma'adanan da Alake ya ambaci an gano su a Kaduna akwao karafan platinum, zinari, nickel, jan karfe, lithium da rare earth elements.
A cewarsa, ingancin ma’adanan da aka gano ya sanya Najeriya cikin kasashen da ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa a kasuwar ma’adanai masu amfani wajen samar da makamashi mai tsafta da fasahohin zamani.
Najeriya ta kara matsayi a fannin ma'adanai
Alake ya ce:
“Wannan ne karon farko da nake sanar da wannan labari a bainar jama’a. Binciken da Hukumar Binciken Kasa ta Najeriya ta tabbatar sun gano wani babban yankin ma’adanai masu daraja a jihar Kaduna.”
“An gano tarin karfe na rukunin platinum tare da zinari, nickel, jan karfe (copper), lithium da rare earth elements masu inganci sosai, wanda zai kara matsayin Najeriya a fannin ma’adanai.”
Ya kara da cewa wani kamfani mai zaman kansa ne ya gano ma’adanan tare da hadin gwiwar NGSA, kamar yadda jaridar Daily Poat ta rahoto.
Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai
Alake ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da gyare-gyare domin bunkasa bangaren ma’adanai da jawo karin masu zuba jari.
Ya bayyana cewa gwamnati ta soke lasisin hakar ma’adanai sama da 3,000 saboda rashin aiki da kuma karya ka’idoji.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Mun mayar da hankali wajen tabbatar da bin doka, gaskiya da kuma tabbatar da cewa masu lasisi suna da niyyar bunkasa ma’adanan da aka ba su.”
An dawo da hakar ma'adanai a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa ministan ma'adanai, Dele Alake, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ɗage haramcin haƙar ma'adanai a jihar Zamfara.
Ministan ya bayyana cewa gaggarumin ci gaban da aka samu a harkokin tsaro a faɗin jihar Zamfara ne dalilin ɗage dokar.
A 2019 ne gwamnatin tarayya ta hana ayyukan haƙar ma'adanai a Zamfara, san nan ta umarci ƴan ƙasashen da ke cikin wuraren haƙar ma'adanai a jihar da su fice daga yankin nan take.
Asali: Legit.ng

