Zaben Cike Gurbi: APC Ta Ci Gaba da Karfafa Ikonta bayan Nasara a Kano
- Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi da aka yi na majalisar wakilai a jihar Kano
- INEC ta jagoranci gudanar da zaben cike gurbin ne bayan rasuwar dan majalisar tarayya, Hon. Muhammad Hassan daga Kano
- Sakamakon ya nuna APC ta samu kujerar mazaɓar Dawakin Kudu/Warawa, bayan sauran ’yan takara sun samu ƙuri’u kaɗan a zaɓen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi da aka yi a Kano.
INEC ta ayyana Rabiu Shuaibu, ɗan takarar jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka yi a jiya Asabar 20 ga watan Yunin 2026.

Source: Facebook
Majiyoyi daga TheCable suka ce an yi zaben ɗan majalisar wakilai na mazaɓar Dawakin Kudu/Warawa da ke bayan rasuwar wanda ke kan kujerar.
An yi rashin ɗan majalisa a Kano
Legit Hausa ta ruwaito cewa Hon. Muhammad Danjuma Hassan ya rasu yana da shekaru 66 a Abuja bayan jinya da ya sha fama da ita.
Kafin rasuwarsa, shi ne ɗan majalisar mai wakiltar mazabar Dawakin Kudu/Warawa a jihar Kano da ake yi wa gogaggen ɗan siyasa.
Kano: An samu sakamakon zaɓen cike gurbi
Farfesa Umar Sani, wanda ya kasance jami’in tattara sakamakon zaɓen, ne ya sanar da sakamakon a ranar Asabar bayan kammala zaɓen da aka gudanar.
An gudanar da zaɓen cike gurbin ne a ranar 20 ga watan Yuni a dukkan sassan mazaɓar Dawakin Kudu da Warawa.

Source: Original
Kano: Kuri'an da ɗan takarar APC ya samu
Bisa ga sakamakon da INEC ta fitar, Rabiu Shuaibu na APC ya samu ƙuri’u 35,356, lamarin da ya ba shi damar zama wanda ya yi nasara.
Lawal Garba Haruna na jam’iyyar APM ya samu ƙuri’u 268, yayin da Abubakar Yahya Muhammad na jam’iyyar LP ya samu ƙuri’u 98, cewar Daily Post.
Da yake sanar da sakamakon, Farfesa Umar Sani ya ce ɗan takarar APC ya cika dukkan sharuddan doka da suka wajaba domin a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Ya ce:
“Rabiu Shuaibu na jam'iyyar APC, bayan ya cika dukkan sharuddan da doka ta tanada, an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar.”
Wannan sakamako ya nuna cewa jam’iyyar APC za ta riƙe kujerar mazaɓar tarayya ta Dawakin Kudu/Warawa a majalisar wakilan tarayya.
INEC ta tabbatar da nasarar APC a Ekiti
An ji cewa hukumar zaɓe ta INEC ta ayyana gwamna mai ci, Biodun Oyebanji na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Ekiti na 2026.
Oyebanji ya samu ƙuri’u 319,224 inda ya kayar da ɗan takarar PDP, Oluwole Oluyede, da na ADC, Dare Bejide a zaɓen da aka kwatanta da wanda aka yi cikin lumana.
Duk da koke-koken BVAS da zarge-zargen magudi daga wasu jam’iyyu, masu sa ido sun yaba da zaman lafiya da yadda zaɓen ya gudana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

