Mambobin JTF 103 sun shiga aikin soja, an basu kudade da filaye
Rundunar sojin Najeriya ta kwashi tsoffin yan banga 103 da suka taimaka wa sojoji wajen yaki da Boko Hara a jihar Borno aiki.
Tsoffin yan bangan wanda aka fi sani da Civilian-JTF sun samu kyauta a yammacin ranar Litinin daga gwamnatin jihar Borno ciki harda kudade da kuma filaye.
Mutane 103 da aka kwasa aiki na cikin rukunin ma’aikatan da aka dauka a hukumar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro.

Asali: Depositphotos
Zuwa yanzusama da mambobin kungiyar Civilian-JTF sama da 400 sun samu shiga rundunar sojin da taimakon gwamnatin jihar Borno.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari, Lalong, Dalung da malaman addini na ganawar sirri
Sabbin daukan, wanda suka dawo gida bayan kammala horonsu a sasanin rundunar sojin Najeriya na suna a gidan gwamnati, Maiduguri a ranar Litinin dominnuna godiyarsu.
Sojojin sun yi godiya ga wamnati da mutanen Borno da suka basu damar yiwa kasarsu hidima.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng
Asali: Legit.ng